Mai dakin Ojukwu ta bada labarin irin halin maƙon Peter Obi na rashin son facaka da kudi

Mai dakin Ojukwu ta bada labarin irin halin maƙon Peter Obi na rashin son facaka da kudi

  • Bianca O. Ojukwu ta bada labarin wata haduwarsu da Peter Obi lokacin ya kawo ziyara a Amurka
  • Da aka kai Obi shago ya saye riga, sai ya nuna kudin rigar (N1.2m a yau), ya yi masa tsada sosai
  • Sai dai Gwamnan ya saye riga mai sauki, a karshe ya bada Daloli domin a taimakawa marasa karfi

Tsohuwar Jakadiyar Najeriya zuwa kasar Sifen, Bianca Ojukwu, ta bada labarin wata haduwarsu da Peter Obi, wanda yanzu yake takarar shugaban kasa.

Bazawarar Marigayi Ojukwu ta yi amfani da shafinta na Facebook ne ta nuna Najeriya ta na bukatar mutum mai matukar tsantsani da rashin facaka.

Wata rana a shekarar 2009, a lokacin yana Gwamna Peter Obi ya kai wa Dim Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu da mai dakinsa ziyara a Dallas, Amurka.

Kara karanta wannan

Mataimakin Atiku: 'Zunuban' Wike, Dalilan Da Yasa Aka Zabi Okowa, Majiya Ta Bayyana Gaskiyar Lamari

Obi ya zo birnin Texas ne domin isar da sakon Goodluck Jonathan, kuma ya halarci taron Dallas Marriot.

Daga shi sai karamin akwati

A cewar Bianca babu abin da Obi ya zo da shi sai wata ‘yar karamar jakar hannu da yake da ita. A ciki babu komai sai tarin takardu da wata rigarsa daya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A nan ne Bianca da Marigayi Ojukwu suka nuna masa bai da rigar kirki da zai je wajen taron da ita. A dalilin haka aka kai shi shagon Nieman Marcus.

Peter Obi
Peter Obi a Legas Hoto: @PeterObi
Asali: Twitter

Ta yi tsada da yawa

Ko da ya isa shagon sai ya ga wata rigar kwat ta kamfanin Tom Ford ta $3985, da Obi ya lissafa kudin a darajar Naira, sai ya nuna shi sam ba zai iya sayenta ba.

Kara karanta wannan

Hotunan Ziyarar Da Kwankwaso Ya Kai Ondo Don Jaje Kan Kisar Masu Ibada 40 a Coci

Gwamna Obi yake cewa kudin rigar zai isa a horar da yara da-dama a Najeriya. Aka buga, amma ya nuna sam ba zai kashe kudi masu yawa a kan rigar ba.

Daga nan aka tafi shagon Steinmart, ya dauki wata riga ta $220, wanda da ita ya je wajen taronsa.

Obi ya bada sadakar $3800

Da aka je yi wa Obi rakiya a jirgi, sai ya fito da $3800 ya ba Misis Ojukwu, ya nemi tayi amfani da kudin domin ta taimakawa marasa karfi da gidauniyarta.

Da kudin aka taimakawa wata mai doya da ta yi gobara, da wata mata maras lafiya. A cewar Bianca Ojukwu irin wannan dabi'ar ce za ta taimakawa Najeriya.

Mbaka ya soki Obi

The Cable ta ce Bianca Ojukwu ta kawo labarin abin da ya faru a 2009 ne biyo bayan sukar da Ejike Mbaka ya yi wa Cif Obi na cewa yana da makon kudi.

Kara karanta wannan

Harin cocin Ondo: Atiku ya bayar da gudunmawar miliyan N10 ga wadanda abun ya ritsa da su

A jiya aka ji shugaban cocin Adoration Ministry a Enugu ya yi hasashen Jam’iyyar LP ba za ta ci zaben 2023 saboda rashin sakin hannun 'dan takaran na ta.

Rabaren Ejike Mbaka ya yi huduba a cocinsa, ya yi kaca-kaca da Peter Obi, ya ce marowaci ne, maras taimakon coci, har da zarginsa da cin amanar APGA.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng