Bidiyon yadda wani Mutumin ya yi cacar cinye naman tukubar tsire, ya shiga wani hali
- Wani ɗan Najeriya ya shiga tsaka mai wuya tare da Mai Tsire bayan gaza cinye naman da suka yi caca a kai
- Rahotanni sun bayyana cewa mutumin ya yi caca da mai suya kan cewa zai iya cinye baki ɗaya naman da ya soya na N22,000
- Sun yi yarjejeniyar cewa ba zai biya ko sisi ba idan har ya cinye naman baki ɗaya, amma lamarin ya canza fuska
Wani mutumi da ya sa caca da Mai Tukubar Tsire ya kare cikin yanayi mara dadi yayin da ya kamu da matsananciyar gajiya da ƙoshi.
A cewar @Gossipmilltv mutumin ya snaya caca da Mai Tsiren cewa zai iya cinye dukkan naman da aka soya lokaci guda.
Yarjejeniyar da suka yi
Da yake amince wa da kalubalen mutumin, Mai tsiren ya yarda da cewa mutumin ba zai biya ko Kwabo ba idan har ya iya cinye naman baki ɗaya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A ɗaya ɓangaren yarjejeniyar kuma sun amince da cewa mutumin zai lale kuɗi ya biya Mai tsire haƙƙinsa idan har ya gaza cinye naman.
Shafin na Istagram ya yi bayanin cewa mutumin ya iya cinye naman N12,500 daga cikin na N22,700, daga nan kuma ya nuna gajiya wa.
A ruwayar @Instablog9ja yayin da suka saka bidiyon sun ce nama ya kai na kimanin naira N25,000.
Yayin da rahotannin biyu suka ci karo da juna kan adadin darajar naman, amma sun rahoto da baki ɗaya cewa mutumin ya shiga gasar da mai tsire.
A bidiyon da ya watsu, mutumin ya shiga matsananciyar gajiya kuma alamun tausayi sun bayyana a fuskarsa. Mai Nama ya cafke rigarsa sakamakon gaza biyan kuɗin naman da ya ci.
Kallo Bidiyon anan ƙasa
Martanin mutane kan abun da ya faru
@Bro_jays ya ce:
"Sai Ƙodar mutum ta yi bindiga yayin kokarin cusa mata wannan abun, wannan lamarin kaɗai zai iya sa Koda ta tashi aiki nan gaba, meyasa bamu san ciwan kan mu bane kan irin ilimin nan, ba mu san abun da zai kawo ƙarshen rayuwar mu ba ko cika shan ruwa ka iya zama guba."
@Freshamor ya ce:
"Idan har ka san abinci da me gina jiki da zaka iya daina cin nama kwata-kwata. Rashin damuwa da abu ba zai bar mutanen mu su san komai ba."
@diva_Ella ya ce:
"Irin wannan gasar nake son shiga, ta ya kuma meyasa shi kuwa ya gaza cinyewa? Nama shi ne abincin da na ƙauna duk da nasan yana da illa ga lafiya."
A wani labarin kuma Ana shirin zaɓen fidda gwanin APC, Babban Hadimin Buhari ya gana da Jonathan a Abuja
Kakakin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari , Malam Garba Shehu, ya gana da tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan.
Shehu ya bayyana cewa dukkan su sun ji daɗi kuma sun nuna wa juna ƙauna a Otal ɗin Fraser Suites Hotel, Abuja.
Asali: Legit.ng