‘Yan bindiga sun tsare mai tsohon ciki, ta na kokarin nakuda, su na neman kudin fansa

‘Yan bindiga sun tsare mai tsohon ciki, ta na kokarin nakuda, su na neman kudin fansa

  • ‘Yan bindiga sun yi ta’adi a Jalingo, har sun yi awon gaba da wasu mutane a makon da ya gabata
  • Akwai wata mai tsohon cikin da haihuwa ko yau ko gobe a cikin wadanda aka yi garkuwa da su
  • Haka zalika ‘Yan ta’adda sun dauke mai shekara 80 da mai juna biyu da aka tare jirgin Abuja-Kaduna

Taraba - A garin Jalingo da ke jihar Taraba, masu garkuwa da mutane sun rike wata Baiwar Allah duk da ganin irin mawuyacin halin da ta samu kan ta.

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa wannan mata mai dauke da juna biyu ta shiga nakuda, amma ‘yan bindigan da suka kama ta sun ki fito da ita.

Asali ma sai aka ji labarin cewa su na neman a aiko masu kudin fansa idan ana so ta samu ‘yanci.

Kara karanta wannan

Farawa da iyawa: Takarar Shugaban kasar da Ngige zai yi a 2023 ta gamu da bakin jini

A ranar Asabar ‘yan bindigan su ka dauke wannan mata tare da wasu mutane shida a garin Jalingo. Wannan abu ya faru ne da kimanin karfe 3:00 na dare.

Rahoton ya bayyana cewa wannan matar ta na zama ne a garin Kano, ta ziyarci iyayenta a jihar Taraba kwanan nan yayin da ta ke shirin haifa masu jika.

Miyagun sun kira mahaifinta a waya, sun bukaci ya yi gaggawar biyan kudin fansa domin ta fara nakuda. Har yanzu dai ‘yan sanda ba su iya cewa komai ba.

Titin jirgin kasa
Wani jirgin kasa a Najeriya Hoto: von.gov.ng
Asali: UGC

Jirgin kasan Kaduna-Abuja

Legit.ng Hausa ta na da labari cewa daga cikin matafiyan da aka tare a jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna a watan Maris, akwai wata mata da ke da tsohon ciki.

Kara karanta wannan

Harin jirgin Abj-Kad: Gwamnatin Buhari ta fara tattaunawa da 'yan bindiga

Badiya Dauda Mani ta yi jimamin abokanta da aka dauke; Aisha da Rashida. Ta ce akwai masu ciki, tsofaffi da ‘yan mata da yanzu suke hannun ‘yan ta’adda.

Da yake magana a shafinsa na Facebook, shi ma wani malamin jami’ar ABU Zaria ya tabbatar da cewa har da mahaifiyarsa mai shekara 80 aka yi gaba a jirgin.

Baya ga wannan tsohuwa, ‘yan bindigan sun hada da ‘yaruwarsa sun yi gaba. Yanzu tsawon makonni uku kenan ba a san halin da mutanen nan ke ciki ba.

Mutum daya kacal ya dawo gida

Jama’a su na cigaba da yin kira ga gwamnati tayi kokari domin a ceto wadannan Bayin Allah. Zuwa yanzu dai mutum daya kurum ake da labarin ya kubuta.

Ana da labari shugaban bankin manoma na kasa watau BOA, Alwan Hassan ya samu ‘yanci daga hannun ‘yan ta’addan da suka yi garkuwa da su kwanan baya.

Kara karanta wannan

Harin 'yan bindiga a Plateau: Ya zuwa yanzu mun binne mutane 106, inji shugaban karamar hukuma

Amma ba haka nan kurum ‘yan ta'addan nan su ka saki shugaban bankin manoman na kasa ba. ‘Yanuwan wannan Bawan Allah sun ce sun biya fansar N100m.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng