Yadda arzikin Dangote ke hawa da sauka cikin shekaru 11 da suka shude
Mujallar Forbes ta sake jerin masu kudin nahiyar Afrika na shekarar 2022, dan Najeriya ne ke kan gaba.
A bisa lissafin mujallar da ta shahara a duniya, arzikin Dangote ya tashi daga $11.5bn a shekarar 2021 zuwa $14bn a 2022.
Attajirin dan kasuwa, dan asalin jihar Kano, Alhaji Aliko Dangote, ya kwashe shekara da shekaru matsayin mutum daya mafi arziki a Afrika.
Hakazalika shine bakin mutum mafi arziki a fadin duniya.
A bisa rahoton Nairametrics, bakin mutum 15 kadai ne biloniya a fadin duniya. Cikinsu akwai yan Najeriya uku kacal.
Ka yadda arzikin Dangote ke hawa da sauka cikin shekaru 11 (2012 - 2022) da suka gabata:
2012: $11.2bn
2013: $16.1bn
2014: $25bn
2015: $14.7bn
2016: $15.4bn
2017: $12.2bn
2018: $14.1bn
2019: $10.4bn
2020:$8.3bn
2021: $11.5bn
2022: $14bn
Forbes ta saki jerin masu kudin duniya na 2022: Dangote ne na 130
Mujallar Forbes ta saki jerin sunayen masu kudin duniya inda takwas daga cikin goman farko yan kasar Amurka ne, sannan daya daga Faransa, dayan kuma daga Indiya.
Har ila yau, Amurka ke da masu kudi mafi yawa inda ta tara bulunoyoyi 735.
Independent UK ta ruwaito cewa Elon Musk wanda shine na daya gaba daya kudin bai wuce $2 billion ba a 2012, amma yanzu ya mallaka $218 billion (sama da N90.61trn).
Asali: Legit.ng