Raya Sunnah: Wani Matashi dan shekara 32 ya Auri mata uku rana daya

Raya Sunnah: Wani Matashi dan shekara 32 ya Auri mata uku rana daya

  • Wani matashi ɗan kasar Kongo, ya Angonce da kyawawan yan matansa uku yan uwan juna a rana daya
  • Matashin ya nuna farin cikinsa da Auren, sannan ya ba da labarin yadda ya jaɗu da baki ɗaya Amaren sa uku
  • Sabbin ma'auratan sun nuna cewa a shirye suke su fuskanci kowane kalubale tun da suna kaunar junan su

DR Congo - Wani matashi mai suna, Luwizo, ya Angonce da tsala-tsalan yan mata uku da suke yan uwa ɗaya a kasar Congo, kamar yadda jaridar Punch ta rahoto.

Angon ɗan kimanin shekara 32 a duniya yace ya haɗu da ɗaya daga cikin matan yan uku mai suna, Natalie, a dandalin Facebook, suka fara fira har ya kai ga soyayya.

Yace bayan sun haɗu Natalie ta gabatar da shi ga yan uwanta mata guda biyu, Nadege da Natasha, ba da jimawa ba suka faɗa soyayya da shi.

Kara karanta wannan

Wani bawan Allah ya daba wa dan Acaba makami har lahira kan ya buge masa Kare a Gombe

Ango da Amarensa guda uku da wasu kawayen Amarya
Raya Sunnah: Wani Matashi dan shekara 32 ya Auri mata uku rana daya Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Angon wanda aka fi sani da Wizo ya ce ya yi matukar mamakin yadda ya haɗu da matan uku daga zuwa maganar aurensa da ɗayansu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daily Trust ta rahoto Ya ce:

"Na yi matukar mamaki, wanda har na kusa faɗuwa na suma, gani na yi abun kamar a mafarki."

Kasanncewar ya matan yan uku ne kuma suna da alaƙa ta kusa da juna, shiyasa suka zabi su auri mutum ɗaya su duka.

Wane farin cikin matan suka yi?

Da aka tambaye su yadda suka ji da lamarin, ɗaya daga cikin Amaren ta ce:

"Da muka faɗa masa ya aure mu baki ɗaya, ya yi mamaki, amma saboda yana kaunar mu duka, ba bu abin da ya kawo mana cikas tun da muna kaunar shi."
"Duk da wasu na ganin ba zai yuwu mata uku su Auri mutum ɗaya mu raba shi ba, a wurin mu amfani da abu ɗaya ya kasance a rayuwarmu tun da muka zo duniya."

Kara karanta wannan

Babu dadi: IGP ya koka kan yadda 'yan sanda ke amfani da makamai ta wasu hanyoyi

Angon ya kara da cewa duk da iyayen shi ba su yadda ba shiyasa ba su halarci ɗaura aurensa ba, amma bai yi dana sanin hukuncin da ya yanke ba.

A wani labarin kuma An tsinci gawar mai haɗa wa Mataimakin shugaban ƙasa takalmi a daki a Abuja

Wani mazaunin yankin ya ce lokacinsa ne ya yi, domin ya kwanta lafiya lau, da safiyar Lahadi aka tsinci gawarsa a daki.

Mataimakin shugaban ƙasa, wanda mamacin ya taba haɗa wa takalma ya yi jajen rasuwarsa a wata sanarwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262