Zamfara: ‘Yan bindiga sun kashe Bayin Allah, sun hana ‘Yan gari yi masu jana’iza har yau

Zamfara: ‘Yan bindiga sun kashe Bayin Allah, sun hana ‘Yan gari yi masu jana’iza har yau

  • Bayan kwanaki hudu da yi wa mutane kisan gilla a Daraga, har yanzu ba a iya yi masu jana’iza ba
  • ‘Yan bindigan da suka yi ta’adin sun ki ficewa daga kauyen, don haka an gagara birne gawawwaki
  • Wani mazaunin yankin ya shaidawa ‘yan jarida cewa duk sun tsere sun bar gidajensu a karkarar

Zamfara - Kwanaki hudu da kashe mutane akalla 12 a kauyen Daraga, mutanen wannan gari a jihar Zamfara sun ce ‘yan fashin daji sun hana ayi masu sutura.

Jaridar Premium Times ta kawo rahoto inda aka ji al’ummar kauyen Daraga a karamar hukumar Maru su na kokawa a game da halin rashin tsaron da suke ciki.

Mutanen da ke zama a yankin sun shaidawa BBC Hausa cewa sun gagara birne ‘yanuwansu da aka hallaka saboda har yanzu ‘yan bindiga sun ki barin garinsu.

Kara karanta wannan

Ronaldo, Ozil, Mane da sauran ‘Yan kwallon kafa da suka fi kowa taimakawa marasa karfi

Wani mutumi da ya zanta da manema labarai ba tare da ya bari an kama sunansa ba, ya bayyana cewa ‘yan bindigan sun kona gidansa, sun bindige mutanensa.

Baya ga ‘danuwansa da aka kashe, wannan mutum ya ce ‘yan bindigan sun harbe ubangidansa a shago.

Gwamnan Zamfara
Gwamna Bello Matawalle da Janar Uwem Bassey Hoto: zmsg.ng
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Halin da mutane su ke ciki

“Yanzu haka da na ke yi maka magana, babu mutum ko daya a wannan kauyen. Dukkanmu mun tsere daga yankin.”
“An tabbatar da cewa an kashe mutane 12, sannan da-dama sun samu rauni a harin. An kashe mani abokai takwas.”
“Kuma ‘yan bindigan su na nan a kewayen karkarar, sun hana mu dauko gawarsu, mu yi masu sutura a birne su.”

- Inji majiyar

Ina jami'an tsaro?

Wannan Bawan Allah ya shaida cewa sun yi kokarin tuntubar jami’an tsaro, amma ba a dace ba. A cewarsa ‘yan bindigan sun fi karfin dakarun da su ke Dan Kurmi.

Kara karanta wannan

Mun shiga uku: Tsadar man fetur ya sa 'yan Najeriya kuka, sunyi zazzafan martani

Majiyar ta ce jama’a sun tsere daga kauyukan Dan Kurmi, Bena, Zargado a jihar Zamfara, haka zalika duk an yi kaura daga yankunan Wasagu da Unashi a Kebbi.

Da aka nemi a tuntubi kakakin ‘yan sandan jihar Zamfara, Mohammed Shehu, bai dauki waya ba.

Siyasar Zamfara

A Zamfara ta siyasa ake yi, inda kwanaki aka ji tsohon ‘dan majalisar Kaura Namoda/Birnin Magaji, Aminu Sani Jaji ya caccaki tsohon gwamna, Abdulaziz Yari

Hon. Aminu Sani Jaji ya bi gwamna mai-ci Bello Matawalle wanda aka damkawa APC, kuma ya ce bai tunanin har yanzu Yari yana da rajistar zama ‘dan jam’iyya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng