Yadda Sanata Dino Melaye ya yi wa dubban mabiya karya ana tsakiyar gasar AFCON

Yadda Sanata Dino Melaye ya yi wa dubban mabiya karya ana tsakiyar gasar AFCON

  • A ranar Asabar, 5 ga watan Fubrairu 2022, Dino Melaye ya wallafa wani bidiyo a shafukan sada zumunta
  • Melaye ya daura bidiyon da sunan magoya bayan kasar Kamaru su na dukan ‘yan wasansu a AFCON
  • Da aka bi diddikin bidiyon, an gano cewa wannan lamarin sam bai faru a wasan Kamaru da Masar ba

Sanata Dino Melaye wanda ya wakilci Kogi ta yamma a majalisar dattawa ya yi ikirarin magoya bayan Kamaru sun jibgi 'yan wasansu a gasar AFCON.

The Cable ta ce hakan na zuwa ne bayan ‘yan kwallon Masar sun doke na kasar Kamaru a gasar cin kofin Afrika a filin wasan Olembe da ke Yaounde.

Bayan an tashi wasan, sai Melaye ya kinkimo wani bidiyo ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya ce magoya bayan su na huce haushinsu a kan ‘yan wasansu.

Kara karanta wannan

Mun shiga uku: Tsadar man fetur ya sa 'yan Najeriya kuka, sunyi zazzafan martani

“Magoya-bayan Kamaru suna jibgar ‘yan kwallonsu saboda sun sha kashi a hannun kasar Masar. Abin takaici.” - Dino Melaye.

Bidiyon ya yi kasuwa

Rahoton ya ce a dalilin Sanatan, bidiyo ya ratsa kafafen zamani. A shafinsa kurum, mutane kusan 500 sun maida martani, mutane 350 sun yi ta yayata sakon.

A dandalin Twitter, mutanen da suka nuna wannan bidiyon ya ba su sha’awa sun haura 1, 000.

Dino Melaye
Sanata Dino Melaye Hoto: @dino_melaye
Source: Twitter

Sama da mutane miliyan 2.8 suke bibiyar tsohon Sanatan a shafinsa na Twitter. Wannan ya sa ya yi tasiri wajen yada bidiyon yayin da ake buga gasar kofin AFCON.

Tsohon ‘dan majalisar ya kuma daura bidiyon a Instagram inda ya samu karbuwa bayan an kalle shi kusan sau 400, 000, an kuma bar masa martani sama da 2, 700.

Yayin da yake da mabiya miliyan 2.2 a Instagram, mutane fiye da miliyan 1.5 suke bibiyar Melaye a Facebook inda a nan ma dubban mutane sun ga bidiyon da ya sa.

Kara karanta wannan

Kwankwaso: Na ki goyon bayan Tofa, Rimi, Buhari na zabi Abiola, Obasanjo da Jonathan

Gaskiyar lamarin

Da The Cable ta bibiyi bidiyon, ta gano ba a wasan hakan ta faru ba. Wanda ya dauki wasan ya ce ba ayi rigima bayan an tashi kwallo tsakanin Masar da Kamaru ba.

Bayan an tashi wasan, magoya-bayan Kamaru sun fita daga filin kwallon Olembe salin-alin ba tare da sun tada tarzoma ba, akasin abin da Dino Melaye ya rubuta.

Bincike ya nuna cewa magoya-baya sun kutso cikin fili ne bayan wasan Aljeriya da Ivory Coast a filin kwallon kafa na Japoma da ke Douala domin nuna farin cikinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng