Raya Sunnah: Kwamishinan jiha ya biya Sadaki, kayan ɗaki, an ɗaura auren marayu 20

Raya Sunnah: Kwamishinan jiha ya biya Sadaki, kayan ɗaki, an ɗaura auren marayu 20

  • Taimakon maraya a Addinin musulunci ya na da falala mai ɗumbin yawa, musamman a irin yanayin da muke ciki
  • Kwamishinan jihar Zamfara ya ɗauki nauyin kayan daki da sauran abubuwan da suka shafi aure, har aka ɗaura auren marayu 20
  • Sarkin Tsafe, Alhaji Bawa, ya yaba wa kwamishinan bisa wannan abun alkairi, tare da rokon ma'auratan su zauna lafiya

Zamfara - Kwamishinan kula da wuraren buɗe ido da harkokin Otal na jihar Zamfara, Alhaji Abubakar Abdullahi, ya ɗauki nauyin komai na ɗaura auren marayu 20 a karamar hukumar Tsafe.

Leadership ta rahoto cewa Sarkin Tsafe, Alhaji Muhammad Bawa, shi ne ya jagoranci ɗaura auren marayun.

Taron ɗaura aure a Zamfara
Raya Sunnah: Kwamishinan jiha ya biya Sadaki, kayan ɗaki, an ɗaura auren marayu 20 Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Sarkin ya yaba wa kwamishina Abdullahi bisa wannan namijin ƙoƙari da yayi kuma ya yi wa ma'aurtan nasiha su zauna lafiya da juna ta hanyar girmamawa da adalci.

Kara karanta wannan

Babu wanda ya isa ya kai tikitin takarar shugaban kasa wani yanki, Sule Lamido ya fusata

Haka nan kuma ya yi kira ga masu kudin yankin su yi koyi da kwamishinan, ta hanyar ɗaukar nauyin aure a matsayin ɗaya daga cikin hanyoyin tallafawa marayu da masu karamin karfi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jawabin Kwamishina a wurin taro

A jawabinsa, Honorabul Abdullahi, yace ya ɗauka matakin ɗaura musu auren ne domin taimaka wa marayu su sami damar raya Sunnah cikin Sauki.

Kwamishinan ya ce:

"Bisa tsadar da rayuwa ta ƙara yi a yanzu, abu ne mai matuƙar wahala marayu da mutane masu ƙaramin karfi su sami damar yin aure cikin sauki."

Mista Abdullahi ya ƙara da cewa an yi tsari me kyau wajen zaɓen marayun da aka tallafa wa da wannan garaɓasa ta Aure.

Legit.ng Hausa ta gano cewa kowane ma'aurata sun samu kyautar kayan ɗaki da suka haɗa da gado, katifa da dai sauran su, da kuma kayayyakin abinci.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Miyagu sun kashe mataimakin kwamishinan yan sanda

A wani labarin ka daban kuma Shugabannin majalisa biyu da wasu yan majalisun PDP uku zasu koma jam'iyyar APC

Da yuwuwar sauya shekar Sanata Emmanuel Bwacha zuwa APC ya zama babban alheri a siyasar jam'iyyar reshen jihar Taraba.

Tsofaffin shugabannin majalisar dokokin Taraba biyu da kuma wasu yan majalisu uku na shirin sauya sheka zuwa APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262