Idan ku na so, na ba ku: Magidanci ya yi alkawarin ba Iyayen Hanifa kyautar ‘yar da ya haifa

Idan ku na so, na ba ku: Magidanci ya yi alkawarin ba Iyayen Hanifa kyautar ‘yar da ya haifa

  • Abdullahi Ahmed Latus ya ce idan iyayen Hanifa sun yarda, to zai ba su kyautar yarinyar cikinsa
  • Wannan mutumi da ke zaune a garin Darazo a jihar Bauchi, ya samu labarin kisan gillar Hanifa
  • Duk da ba su hada jini ko wata dangantaka ba, wannan mutumi ya shirya mallakawa iyayen ‘yarsa

Bauchi - An samu wani Bawan Allah mai suna Abdullahi Ahmed Latus, da ya fito ya bayyana niyyarsa na taimakawa iyayen Hanifa Abubakar.

Labarin da muka samu daga Facebook ya bayyana cewa Abdullahi Ahmed Latus mai zama a jihar Bauchi, ya yi alkawarin bada kyautar ‘yar cikinsa.

Malam Abdullahi Latus da ke zaune a garin Darazo, ya bayyana cewa idan iyayen wannan yarinya da aka kashe su na da bukata, zai ba su madadinta.

Kara karanta wannan

Takarar shugaban kasa a 2023: Babatu 3 da Tinubu ya yi da ka iya sa ya fadi a 2023

Wani ‘dan jarida a Kano, Abba Gwale ya kawo labarin wannan mutumi a shafinsa na Facebook.

Abba Gwale yana aiki ne a gidan rediyon Nasara Radio 98.5 FM da ke Kano, kuma edita ne na sashen wasanni a gidan jaridar nan ta Leadership Hausa.

“Wannan mutumin mai suna Abdullahi Ahmed Latus, daga garin Darazo na jihar Bauchi, yayi alkawarin zai bawa iyayen Hanifa 'yarsa ta cikinsa idan har sun amince zasu karba. Kuma mun yi waya dashi ya tabbatar min da niyyar tasa.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

- Abba Gwale

Iyayen Hanifa
Makwafin Hanifa Abubakar Hoto: Abba LG
Asali: Facebook

An ji ta bakin uwar yarinyar?

Amma irinsu Hussaina Sufyan Ahmed su na ganin bai dace wannan mutumin ya dauki shawara haka kurum ba tare da an ji ta bakin mai dakinsa ba.

Malam Salim Toro ya na da wannan ra’ayi, ya ce dole sai an yi magana da mahaifiyar yarinyar.

Kara karanta wannan

Jami'ai sun kyauta: Buhari ya yi martani kan kame mai malamin da ya sace Hanifa

“Menene fa'idar yin hakan? Shin Uwar yarinyar ta amince da hakan ne? Idan ma Uwar ta amince, shin hakan zai mayar da gurbin hanifa a wajen Uwarta ne? Ni a shawara ta da yayi hakuri yabar yarinya a gaban Uwarta gaskiya.”

Haruna Yakubu Guri ya ce baya ga haka, dole sai an yi bincike da kyau kafin a bada kyautar yaro, ka da a je a jefa karamin yaro cikin wani mawuyacin hali.

A wani dalili?

Wasu da-dama sun ce babu dalilin ayi kyauta da yarinya domin ta maye gurbin Hanifa da aka kashe, tun da iyayen wannan yarinya ba su daina haihuwa ba.

“Dan Allah yayi hakuri. Ya bar yarsa a gurinshi ya riqa Taya Su da Addua Allah ya Basu wata. Sai Dai in mahaifiyar yarinyar ba ta da Rai to da dan sauki.”

- Kauthar Bawa

“Wannan kyautar fa baza ta musanya musu Haneefa ba, jininka shine naka, gara ya rike 'yar shi kawai kada ma nan gaba azo ayi ta rigima.”

Kara karanta wannan

Shugaban makarantar su Hanifa ya magantu: Da gubar beran N100 na kashe ta

- Kabiru Garba

“Ni kuwa gani nake tun da iyayen Hanifa ba haihuwa suka daina ba, a ƙyale su Allah da ya karba ya ba su wata. Idan aka raba yarinyar nan da mahaifiyarta a wannan shekarun, kamar da cutarwa fa.”

- Habib Sani Galadima

Abullahi Yakassai cewa ya yi:

“Bahaushe me ban haushi... In dai ba Yan'uwansa ba Ina za ayi haka.”

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel