Namijin Kishi: Wani magidanci ya dabawa makocinsa wuka har lahira saboda yana soyayya da matarsa
- Wani maigida a jihar Legas, ya fusata da jin labarin cin amanarsa da makocinsa ke masa, ya daɓa masa wuka har lahira
- Rahoto ya bayyana cewa magidancin ya gano makocinsa ya kulla alaƙa da matarsa, kuma suna cin amanarsa a bayan idonsa
- Hukumar yan sanda ta baza komar neman magidancin, wanda ya tattara kayansa ya gudu tare da matarsa
Lagos - Wani magidanci mai suna, Keke, tare da matarsa sun yi batan dabo, bayan zargin Keke ya daɓa wa makocinsa Tela, Daniel, wuka har lahira a yankin Iwaya ta jihar Legas.
Punch ta tattaro cewa, Keke, ya dawo daga aiki wata rana, ɗaya daga cikin maƙotansa ya sanar da shi wata boyayyar alaƙa dake gudana a bayan idonsa tsakanin matarsa da Daniel.
Sai dai wannan labari ya yi matukar fusata Keke, wanda hakan yasa ya fito daga cikin gidansa domin ya kalubalanci Daniels.
Rahoto ya bayyana cewa Keke ya yi wa Telan barazana da wuka, wanda hakan yasa ya tsere domin ɓuya a cikin gidan da yake zaune.
Amma duk da haka, Keke bai hakura ba, sai da ya bi Mista Daniel har cikin ɗakin da ya buya, ya daɓa masa wuka a ƙirji.
An yi gaggawar kai Daniel Asibiti domin ceto rayuwarsa, amma likitoci suka tabbatar da ya mutu da misalin ƙarfe 11:00 na dare, ranar Litinin.
Keke da kuma matarsu, sun tsere daga gidan da suke zaune domin gudun fusatattun mutane su farmake su.
Wane mataki hukumar yan sanda ta ɗauka?
Kakakin rundunar yan sanda ta jihar Legas, CSP Adekunle Ajisebutu, ya tabbatar da faruwar lamarin, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Yace:
"Bamu yi wata-wata ba, muna samun rahoto jami'an mu na caji ofis ɗin Sabo suka dira wurin. An kai mutumin Asibitin dake kan hanyar Harvey, a Yaba domin kula da lafiyarsa, amma ya mutu ana cikin haka."
"Kwamishinan yan sanda, Hakeem Odumosu, ya bada umarnin maida lamarin sashin binciken manyan laifuka na kisan kai, domin gudanar da aikin su."
Kazalika kwamishinan yan sandan ya umarci jami'ai su yi duk me yuwuwa domin tabbatar da sun cafke wanda ake zargi bayan ya tsere.
A wani labarin kuma Sojoji sun yi wa yan bindiga kwantan bauna, sun bude musu wuta a Kaduna
Dakarun sojin Najeriya sun dakile wani hari kuma suka hallaka yan ta'adda biyar a kauyen Kwanan Bataro, karamar hukumar Giwa, jihar Kaduna.
A bayanan da muka samu, sojojin na aikin sintiri a ƙaramar hukumar Giwa yayin da suka samu sahihin bayanin sirri na motsin yan bindiga zuwa garin Fatika.
Asali: Legit.ng