Sai da na ajiye waya a gefe – ‘Dalibar da tayi fice a Jami'ar Al Hikmah ta fadi sirrin nasararta

Sai da na ajiye waya a gefe – ‘Dalibar da tayi fice a Jami'ar Al Hikmah ta fadi sirrin nasararta

  • Kaosarah Abisola Oyesiji ce ta zama gwarzuwar ‘daliba a sashen akanta a Jami’ar Al-Hikmah, Ilorin
  • Da aka kira Kaosarah Abisola Oyesiji domin a ba ta kyauta, hawaye ya zubo mata a gaban mutane
  • Kafin ta yi wannan dace, sai da Kaosarah Oyesiji ta ajiye wayar salula a gefe lokacin jarrabawa

Kwara - Kaosarah Abisola Oyesiji ita ce dalibar da ta yi fice a jami’ar nan ta Al-Hikmah, Ilorin, jihar Kwara a shekarar nan, ta kammala karatu da maki 4.59.

Jaridar Daily Trust ta rahoto Kaosarah Abisola Oyesiji tana bayanin irin sadaukar da rayuwarta ta da tayi domin ganin ta samu gagarumar nasara a jarrabawarta.

A kaf sashen koyon ilmin akanta, Kaosarah Abisola Oyesiji ce ta zama gwarzo a shekarar nan.

Kara karanta wannan

Shehu Sani: 'Yan bindiga sun zama jiha mai zaman kanta a cikin jihohin Arewa maso Yamma

Kafin ta samu wannan nasara, sai da tayi watsi da wayar salularta, sannan kuma ta daina bibiyar shafukan sada zumunta na tsawon watan da su ke jarrabawar.

Ta fashe da kuka

Rahoton yace da aka kira sunanta a matsayin dalibar da ta kammala digiri a fannin akanta da makin da ya fi na kowa, Kaosarah Oyesiji ta fashe da kuka a fili.

'Dalibar Al Hikmah
Kaosarah Abisola Oyesiji Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

“Sai da na sha wahala sosai a rayuwa, amma na godewa Allah (SWT) na ni’imar da ya yi mani wajen ganin cewa ban yi wahalar banza ba.”
“Duk da na yi addu’a kuma a kullum shirye nake da in kara ilmi, na sadaukar da rayuwa ta wajen ganin na cin ma wannan nasara da na samu.”

- Kaosarah Abisola Oyesiji

Kara karanta wannan

Innalillahi: Mummunar gobara ta yi kaca-kaca da wani gida, uwa da jaririnta sun kone a Kano

Wannan Baiwar Allah take cewa su na shafe makonni biyu su na jarrabawa, saboda haka sai ta ajiye wayarta na tsawon makonni shida a wajen wani malaminsu.

Na san abin da na ke yi

“‘Yan ajinmu sun yi ta suka ta, amma na fada masu na san abin da nake hari. Kafofin sada zumunta su na da amfani, amma su na shafar karatu.”
“Abin da na yi imani shi ne ka da in yi amfani da waya na wata daya, kuma in daina bibiyar kafofin sada zumunta. Nagode Allah, na kuma dace.”

- Kaosarah Abisola Oyesiji

Opera News ta rahoto Kaosarah ta na cewa ta na da abokai maza da-dama, amma ba ta bari dangantakar da ke tsakaninsu ta hana ta maida hankali sosai ba.

Amina Mohammed ta zarce

A ranar Litinin ne aka ji cewa António Guterres ya sake zaben Amina J. Mohammed ta cigaba da rike kujerar sakatariyar mataimakiyar majalisar dinkin Duniya.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun sace wani shugaban kwastam mai ritaya a gonarsa a Kwara

Da take magana a Twitter, tsohuwar Ministar Najeriyar, Amina J. Mohammed ta tabbatar da cewa ta karbi wannan mukamin, kuma za ta yi bakin kokarinta a UN.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng