Dukiyar Abdulsamad Rabiu ta karu da $1.9b, ya doke kusan kowa, Dangote kadai ya rage

Dukiyar Abdulsamad Rabiu ta karu da $1.9b, ya doke kusan kowa, Dangote kadai ya rage

  • Ana ganin cewa Alhaji Abdul Samad Rabiu ya zama na biyu yanzu a rukunin masu kudin kasar nan
  • Abdul Samad Rabiu ya mallaki sama da Dala biliyan 7, kusan Naira tiriliyan 3 ya ba baya kenan
  • Attajirin ya yi kudi ne a sakamakon sa hannun jarin kamfaninsa na BUA a kasuwa a farkon 2021

Nigeria - A makon nan ne kamfanin BUA Foods Plc da Alhaji Abdul Samad Rabiu ya mallaka ya samu damar saida hannun jarinsa ga masu sha’awa a Najeriya.

Wani rahoto da Billionaires Africa a fitar ya nuna cewa a sakamakon sa hannun jarin kamfanin BUA da aka yi a kasuwa, dukiyar Abdul Samad Rabiu ta nunku.

Daga Dala biliyan 5.3 a kwanaki, ana maganar arzikin Rabiu ya haura Dala biliyan 7.2 yau.

Kara karanta wannan

Bashin China: Ko yanzu muke bukatar bashi, za mu sake karbowa, Buhari

Wannan zabura da attajirin ya yi a farkon shekarar nan ta sa ya sha gaban Mike Adenuga a jerin masu kudin Najeriya, Adenuga ya mallaki fam Dala biliyan 6.6.

Mike Adenuga wanda ya kafa kamfanin Globacom Nigeria ya dawo na uku a wannan jerin.

Abdussamad Rabiu
Alhaji Abdul Samad Rabiu Hoto: www.ivory-ng.com
Asali: UGC

BUA ya yi daraja

A 1998 ‘dan kasuwan ya kafa BUA Group. A yanzu kamfanin ya saida hannun jari biliyan 18 kan N40, hakan ya sa aka yi wa kamfanin daraja na kusan N720bn.

An sa hannun jarin kamfanin a kasuwa ne kimanin wata guda da BUA ya tattara kasuwancin sukari, mai, fulawa, shinkafa da na taliyarsa duk a wuri guda.

Kaimin da wannan babban kamfanin Najeriya ya yi ya taimakawa Rabiu wajen kara fam Dala biliyan 1.9 a dukiyarsa. A kudin gida, adadin ya kusa N800bn.

Kara karanta wannan

Yari, Modu Sheriff, Al-Makura da jerin mutum 10 masu harin shugabancin APC a zaben 2022

Abdussamad ya yi gaba

Mai kudin ya mallaki kashi 92% na hannun jarin kamfanin simintinsa wanda darajarsa ta kai $5.3bn. Hakan yana nufin yana bin kamfanin Dangote a baya.

Da yake bayanin abin da ya sa suka dunkule kasuwancin a wuri guda, mai kamfanin na BUA yace hakan zai taimaka wajen magance matsalar karancin abinci.

‘Dan kasuwar yace mutane da-dama ba su san irin karfin da BUA ya yi ba, don haka suka tattara komai a wuri guda domin jama’a su rika yaba masu da kyau.

BUA ya yi alheri

Kwanaki aka ji Alhaji AbdulSamad Rabiu, ya ba jami’ar Maiduguri, gudumuwar makudan kudi. Rahoton yace attajirin ya ba jami'ar ta UNIMAID kyautar N1bn.

Mataimakin darektan sashen yada labarai na jami’ar tarayyar da ke garin Maiduguri, jihar Borno, Alhaji Moh’d T. Ahmed ne ya bada wannan sanarwa a 2021.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng