Matashi ya biya abokinsa N100,000 ya kashe mahaifinsa saboda ya gaji da jiran gado
- Dakarun ‘yan sanda sun kama wani Abubakar Mohammed Buba da zargin kashe mahaifinsa a Neja
- Abubakar Mohammed Buba ya amsa laifin da ake zargin sa da aikatawa na kisan tsohon na sa a Chanchaga
- Buba ya yi wannan aika-aika ne saboda ya yi gaggawar cin gadon mahaifinsa mai shekara 52 a Duniya
Niger - Rundunar ‘yan sandan Najeriya na reshen jihar Neja sun kama wani matashi mai suna Abubakar Mohammed Buba da laifin kashe mahaifinsa.
Jaridar Punch tace ‘yan sanda na zargin wannan matashi Abubakar Mohammed Buba mai shekara 25 da hannu wajen hallaka tsohon da ya haife shi.
Ana tuhumar Abubakar Mohammed Buba da biyan wani abokinsa kudi N110, 000 domin ya kashe mahaifinsa, wannan ya faru ne a Chachanga, a jihar Neja.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun yace Bida ya amsa laifinsa, yace ya yi haka ne saboda ya ci gadon dukiya.
A jawabin da DSP Wasiu Abiodun ya fitar a ranar Alhamis, ya bayyana yadda aka tsinci gawar marigayin da wanda aka biya kudi domin ya aika shi barzahu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya amsa laifinsa - NPF
“Ya yi ikirarin ya yi wannan laifi ne saboda ya yi maza ya gaji dukiyar mahaifinsa.” - Wasiu Abiodun
Mai magana da yawun bakin jami’an tsaron yace an kashe Mohammed Buba mai shekara 52 a Duniya, aka kuma jefar da gawarsa a cikin leda a wata bola.
Rahoton da Tribune ta fitar a ranar 6 ga watan Junairu, 2022 yace matashin ya kai ‘yan sanda har zuwa inda aka jefar da gawar mahaifin na sa a Tagwai-Dam.
Wanda ya yi kisan ya tsere
Wannan matashi da ya shiga hannun hukuma yace ya dauki hayar wani Aliyu Muhammed ‘dan shekara 26, ya taimaka masa wajen kashe mahaifin na shi.
Buba ya kuma biya Mista Aliyu Muhammed kudi N100, 000 domin ya yi wannan danyen aiki. Yanzu haka ana neman Muhammed, amma an rasa inda yake.
Jalo Jalingo ya dakata - JIBWIS
Dazu ku ka ji cewa malaman kungiyar Jama’atul Izalatil Bid’ah Wa Iqamatis Sunnah sun yi zama na musamman da Sheikh Ibrahim Jalo Jalingo a garin Abuja.
An yi wannan tattaunawa ne a dalilin karatun da Dr. Jalo Jalingo yake yi kan makomar iyayen Annabi SAW, inda aka umarci ya rufe wannan shafi mai sabani.
Asali: Legit.ng