Tsohon masoyin shahararriyar ‘Yar fim ya karbe motarsa bayan an yi mummunar rabuwa a fili
- Tsohon saurayin Tonto Dikeh, Prince Kpokpogri ya karbe wata motarsa da ke hannun ‘yar wasar
- A shafinsa na Instagram, Kpokpogri ya tabbatar da cewa wannan mota Lexus SUV ta dawo hannunsa
- Hakan dai ya faru ne bayan ‘dan siyasar ya rabu da budurwar ta sa a wani irin kazamin yanayi kwanaki
Delta - Prince Kpokpogri wanda a da yake tare da tauraruwan ‘yar wasar kwaikwayo, Tonto Dikeh, ya karbe wata motarsa da ta dade a hannunta.
Legit.ng ta samu labari cewa bayan wata da watanni ana ta rigima kan abu daya, Prince Kpokpogri ya yi nasarar karbe wannan mota Lexus SUV.
Idan za a iya tunawa, a baya Kpokpogri mai shekara 37 ya zargi Tonto Dikeh da rike mabudin motarsa, duk da kowa ya kama hanyar gabansa a yanzu.

Kara karanta wannan
Uwar 'Yan Crypto: Matar da ta ajiye aiki, ta rungumi Crypto, ta koma samun N30m a wata
Bayan ‘dan siyasar na Delta ya rabu da Dikeh wanda ta shahara a Nollywood, kowanensu ya zo dandalin sada zumunta, ya na maganganu marasa dadi.

Source: Instagram
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kpokpogri ya tabbatar da karbe motarsa
A wani gajeren bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Instagram, an fahimci cewa wannan mutumi ya samu ya karbi mabudin motarsa, har ya tuka abinsa.
Za a ga Kpokpogri ya na murmushi, ya na gaida mabiyansa a wannan bidiyo da yake yawo.
Da wata Baiwar Allah tayi masa magana, ta na taya shi murna, Kpokpogri ya tabbatar da cewa ya karbe wannan motar mai tsada a hannun Dikeh.

Source: Instagram
Martanin masoya a shafukan zumunta
Tuni mabiya da masoya su ka fara tofa albarkacin bakinsu a game da wannan lamari bayan ganin bidiyon ya karade dandalin sada zumuntan.
“Mutum ya karbe kayansa ma abin murna ne, ba kowa zai iya ba.”
- Cjazter
"Na tabbata Poko ta karbe na ta kayan kafin ta bada motar nan."
- Uddiegirl:
"Ita ma Tonto ta karbi motarta Hilux. An yi daidai kenan. Kuma za ma ta iya sayen biyar na irin wannan Lexus."
- Mariam_adun
Mutuwar aure da ake samu
A shekarar nan, igiyar aure da yawa sun tsinke, daga cikin wadanda abin ya shafa har da fitattun attajirai da shaharrun taurarin da ake ji da su a Duniya.
A 2021 aka ji cewa babu aure tsakanin Sani Danja da Mansurah Isah. Haka zalika Bill Gates da Melinda Gates da suke tare tun 1987 sun rabu kwanaki.
Asali: Legit.ng
