Dan crypto ya koma tsince-tsince yayin da mahaifiyarsa ta jawo masa asarar biliyoyi

Dan crypto ya koma tsince-tsince yayin da mahaifiyarsa ta jawo masa asarar biliyoyi

  • Wani mai kudin Bitcoin ya bayyana bacin ransa kan yadda ya koma gida ya tarar mahaifiyarsa ta jefar kwamfutarsa dauke da Bitcoin
  • Ya bayyana cewa yana daya daga cikin wadanda suka sa hannun jari na farko a Bitcoin kuma ya manta ya saka kudinsa
  • Ya fahimci shi attajirin Bitcoin ne bayan ganin abokinsa da suka saya tare ya tsallake da makudan kudade

Wani dan crypto ya tsala ihu yayin da yayi ikirarin cewa mahaifiyarsa ta jefar da na'urarsa Laptop da ta lalace, wanda ke dauke da crypto da darajarsu ta kai dala miliyan 557 (N234 biliyan).

Ya bayyana bakin cikinsa a kafar Reddit, wani dandalin sada zumunta, yana mai cewa shikam dai an gama da rayuwarsa.

Tafka asarar biliyoyi na Bitcoin
Dan crypto ya koma tsince-tsince yayin da mahaifiyarsa ta jawo masa asarar biliyoyi | Hoto: GettyImages
Asali: UGC

A cewar jaridar The Sun UK, ya sayi Bitcoin guda 10,000 a matsayin gwaji a farkon 2010, ya biya kusan dala 80 bayan abokansa na karatun digiri sun rinjaye shi ya saya, ya adana makullin kudin a kwamfutarsa bayan ya tura su daga alkalamin ajiyar bayanai na USB.

Kara karanta wannan

Mutumin da aka kora daga makaranta ya mallaki N32trn, ya zama mafi arziki a China

Yayin da shaharar musayar crypto ke karuwa, ya ce ya tuna da kadararsa ya shiga nemansa, ya yi imanin cewa kakarsa ganin yadda Bitcoin ke kara hauhawa.

Da ya dawo gida don ya nemo tsohuwar kwamfutarsa da ta lalace tsawon shekaru, sai ya ce ya gano mahaifiyarsa ta shiga dakinsa ta jefar da kwamfutar.

Ya ba da labarinsa

Marubucin da ba a san sunansa ba ya rubuta cewa:

"A zahiri na suma, na yi fushi, na rude, na gigice, cikin bacin rai, bakin ciki, fushi da sauransu."

Ya kara da cewa bala’in da ya faru ya sa shi ya samu “karayar zuciya” kuma yana fama da bakin ciki “kowace rana” kamar yadda yake tuna abin da watakila zai samu.

Ya bayyana cewa ya kuma ji haushin mahaifiyarsa, inda ya dora mata laifin jefar da kwamfutar, wacce ta kwashe shekaru tana zaune a cikin tarin “sharar da ba a taba ba.”

Kara karanta wannan

Masu yi da gaske: Bidiyon wani mutum yana yiwa matarsa kyautar jirgi ya jawo cece-kuce

Duk da kokarin da ya yi na ganin rayuwarsa ta dawo daidai, ya yi ikirarin cewa hauhawar farashin Bitcoin na kara dagula masa bakin ciki.

Ya kara da cewa:

"Har yanzu a talauce nake, har yanzu ina zaune tare da iyayena, ina aiki, amma ba wanda nake so ba, kuma ina da abokai, amma ba ma yawan magana, rayuwa ta ki dawowa kamar yadda take da."

Daga karshe dai ya ce ya bar aikin komai saboda halin bakin ciki da yake ciki.

Wanda yace shi ya kirkiro Bitcoin ya gagara cire kudi a asusu a kasuwar Crypto

A wani labarin, Craig Wright, wanda ya ayyana kansa a matsayin wanda ya kirkiri Bitcoin, yana shirin kaura zuwa wani kauye bayan ya ci nasara a kotu inda ya ce an ayyana shi a matsayin wanda ya kirkiro bitcoin.

Duk da yanke hukuncin, al'ummar Bitcoin ba su gamsu ba kuma sun kalubalance shi da ya aika wani kaso na Bitcoin miliyan 1.1 da ya ce yana da ikon akai zuwa wani asusu don nuna ikon mallakarsa.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya gano masu daukar nauyin ta'addanci a jiharsa, ya saka ranar fallasa su

Indiatimes ta ce al'ummar Bitcoin ba su amince da Wright ba, kuma mutane da yawa sun nemi kawai ya motsa wani dan karamin kaso na Bitcoin kamar miliyan 1.1 zuwa wani asusu na daban don tabbatar da mallakar tsabar, lamarin da ya faskara ya zuwa yanzu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Tags: