Bayan shekara 65 a kan gadon sarauta Sarkin Ban Kano, Adnan Mukhtar ya rasu a daren Juma'a

Bayan shekara 65 a kan gadon sarauta Sarkin Ban Kano, Adnan Mukhtar ya rasu a daren Juma'a

  • A daren Juma’ar nan Sarkin Ban Kano, Adnan Mukhtar ya rasu a wani asibiti da yake faman jinya
  • Sarkin Bai ya hau kujerar Hakimin kasar Dambatta a 1954, a lokacin Muhammadu Sanusi I ya na Sarki
  • Alhaji Adnan Mukhtar ya na cikin dattawan Arewacin Najeriya, ya rasu ya na da shekara 95 a Duniya

Kano - A ranar Juma’a, 3 ga watan Disamba, 2021, aka samu labarin rasuwar Sarkin Ban Kano, Mukhtar Adnan, wanda ya na cikin dattawan Arewa.

BBC Hausa ta fitar da rahoton rasuwar Alhaji Mukhtar Adnan dazu da safe. An bayyana cewa Sarkin Bai ya cika ne da tsakar dare, kafin asubar yau.

Daya daga cikin manyan ‘ya ‘yan Alhaji Adnan, Baba Ado ya tabbatarwa ‘yan jarida hakan.

Kamar yadda muka samu labari, Sarkin Bai ya yi fama da rashin lafiya, inda aka kwantar da shi a asibitin UMC Zahir a unguwar Jan-bulo, garin Kano.

Kara karanta wannan

Lokacin mu ne: ‘Dalibin Jami'a mai shekara 28 zai yi takarar Shugaban matasa a Jam’iyyar APC

Za ayi jana’izar marigayin bayan sallar Juma’a a masallacin Juma’a na Dambatta, jihar Kano, inda nan ne mahaifarsa. Sarkin Bai ya rasu ya na shekara 95.

Adnan Mukhtar
Muhammadu Sanusi II da Sarkin Bai Hoto: @Shamsudden M. Danhaki/Facebook
Asali: Facebook

Shekara 65 a sarauta

BBC Hausa ta ce an haifi marigayin shekaru 95 da suka wuce, a watan Janairun shekarar 1926. A gaban idanunsu sai da aka yi sarakuna har shida a Kano.

A shekarar 1954, Sarkin Kano na wancan lokaci Mai martaba Muhammadu Sanusi I ya nada shi a matsayin Sarkin Ban Kano kuma Hakimi a Dambatta.

Sarkin Bai ya na cikin majalisar masu nada Sarki, kuma a karkashinsa ne aka samu sarakuna da-dama a Kano, daga ciki akwai Sanusi I da Ado Bayero.

Aikin gwamnati a baya

Marigayin ya taba zama ‘dan majalisar wakilai a jamhuriyya ta farko a karkashin jam’iyyar NPC. Bayan nan kuma ya rike kwamishinan ilmi na jihar Kano.

Kara karanta wannan

Sanusi: Gwamnati ta bayyana mataki na gaba bayan tsohon Sarki ya yi nasara a kan ta a kotu

Cikin ‘ya ‘yan mamacin akwai Dr. Mansur Mukhtar wanda ya yi Ministan kudi a gwamnatin Yar’adua, yanzu babba ne a bankin musuluncin Duniya.

Sabaninsa da gwamnati a 2019

A baya an ji cewa ya na cikin wadanda suka samu sabani da gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje bayan a dalilin raba masarauta da aka yi zuwa gidaje biyar.

Hakimin Danbatta, Alhaji Adnan Mukhtar, ya fada karkashin sabon Sarkin Bichi (Aminu Ado Bayero) bayan gwamnatin Ganduje ta kacancana masarauta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng