Bichi: Aminu Ado ya sauke Sarkin Bai, daya daga cikin wadanda suka nada marigayi Ado Bayero sarki

Bichi: Aminu Ado ya sauke Sarkin Bai, daya daga cikin wadanda suka nada marigayi Ado Bayero sarki

Masarautar Bichi, daya daga cikin sabbin masarautun da gwamnatin jihar Kano ta kirkira, ta sanar da dakatar da manyan hakimai guda biyar da har yanzu basu yi mubaya'a ga sabon sarki, Aminu Ado Bayero, ba har yanzu.

Manyan hakiman guda biyar da wannan hukunci ya shafa sun hada da hakimin Dambatta, Mukhtar Adnan, hakimin Minjibir, takwaransa na Dawakin Tofa da kuma na Bichi. An sanar da dakatar da hakiman ne bayan kammala zaman fada na ranar Lahadi, 15 ga watan Disamba.

Kazalika, an maye gurbin manyan hakiman nan take, ba tare da wani bata lokaci ba.

Sabbin hakiman da aka sanar da nada, domin maye gurbin wadanda aka tube, sune kamar haka; Abdulhamid Ado Bayero a matsayin sabon hakimin Bichi, Ma'awuya Abbas Sanusi a matsayin sabon hakimin Tsanyawa, Dakta Abdullahi Maikano Rabi'u a matsayin sabon hakimin Dawakin Tofa, sai tsohon haimin Makoda, Alhaji Wada Waziri, a matsayin sabon hakimin Dambatta, da kuma Malam Isma'il Sarkin Fulani a matsayin sabon hakimin Minjibir.

Bichi: Aminu Ado ya sauke Sarkin Bai, daya daga cikin wadanda suka nada marigayi Ado Bayero sarki

Sarkin masarautar Bichi, Aminu Ado Bayero
Source: Facebook

Alhaji Labaran Abdullahi zai maye gurbin tsohon hakimin karamar hukumar Makoda da aka nada a matsayin sabon hakimin Dambatta.

Sanarwar ta kara da cewa nadin sabbin hakiman ya fara aiki daga ranar da sanarwa ta fita, watau Lahadi, 15 ga watan Disamba, 2019.

DUBA WANNAN: Aiyukan alherin marigayi Sani Abacha guda biyar da kwata - kwata ba a maganarsu

Daya daga cikin hakiman da aka sauke, Mukhtar Adnan, ya zama mamba a majalisar nada sarkin Kano a shekarar 1954, kuma yana daga cikin wadanda suka nada tsohon sarkin Kano, Marigayi Ado Bayero, a shekarar 1964, kamar yadda gidan radiyo mai zaman kansa a Kano, Dabo FM, ya sanar.

Ana tunanin cewa hakiman da aka tube din suna cigaba da biyayya ne ga sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, wanda yake yaki da kirkirar sabbin masarautu a jihar Kano.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel