Jami’an tsaro sun kama matar da ta rufe ‘yar shekara 6 a daki na wata da watanni
- ‘Yan sandan jihar Osun sun kama wata mata da ta rufe karamar yarinya na tsawon watanni a gida
- Rahotanni sun ce Olanrewaju Adenike ta garkame wata ‘yar shekara shida ne a wani kazamin daki
- Makwabtanta a Isale-Osun sun samu labarin abin da yake faruwa, sai su ka sanar da jami’an tsaro
Osun - Rundunar ‘yan sandan Najeriya na reshen jihar Osun, sun ceto wata karamar yarinya mai suna Aishat Taiwo daga hannun mai kula da ita.
Daily Trust ta kawo rahoto a ranar Laraba, 1 ga watan Disamba, 2021 cewa wannan mata mai suna Olanrewaju Adenike ta tsare Aishat Taiwo a daki.
Adenike ta rufe wannan yarinya mai shekara shida a cikin wani kazamin daki na tsawon watanni, an ce dakin ya na kusa da wani kewaye.
Jaridar ta rahoto Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Osun, Wale Olokode, yana cewa Olanrewaju Adenike ta gallazawa Taiwo azaba kafin ta kubuta.
Olokode ta bakin mai magana da yawun bakin rundunar ‘yan sanda na Osun, Yemisi Opalola ya bayyana yadda asirin wannan Baiwar Allah ya tonu.
Ceto ya zo wa Aisha Taiwo
Wasu mutane ne suka sanar da jami’an ‘yan sanda game da irin azabar da Olanrewaju Adenike ta ke yi wa wannan yarinya da ta rufe a cikin gidanta.
Makwabtan wannan mata da yanzu ta ke hannu a unguwar Isale-Osun, a yankin Osogbo a jihar Osun ne suka sanar da ‘yan sanda halin da ake ciki.
Halin da yarinyar ta ke ciki
Mai girma kwamishinan ‘yan sanda, Olokode ya shaidawa manema labarai cewa yarinyar ta na hannunsu a halin yanzu, kuma ta na samun kulawa.
Baya ga haka, CP Olokode ya tabbatar da cewa rundunar ‘yan sanda na jihar Osun, su na kokarin gano iyayen ta domin a maida ta karkashin kulawarsu.
Ba a ji ta bakin wannan mata domin sanin abin da ya sa ta yi wannan aiki ba, kuma ‘yan sanda ba su yi bayanin irin matakin da za su dauka a kanta ba.
Masu garkuwa da mutane
A garin Zaria, jihar Kaduna, an ji 'yan bindigan da suka yi garkuwa da wasu ma'aikata sun fito da mutum 10, an tsare 3 saboda ba su cika sharuda ba.
Miyagun ‘Yan bindigan sun ce ba za su saki mutanen da suka sace a garin Giwa ba sai an ba su kudi Naira miliyan 40 da kuma sababbin babura uku.
Asali: Legit.ng