Wata mata ta tashi da sama da Naira miliyan 5 daga ajiya sannu a hankali a cikin asusu

Wata mata ta tashi da sama da Naira miliyan 5 daga ajiya sannu a hankali a cikin asusu

  • Wata mutumiyar Najeriya ta gigita mutane a dandalin sada zumunta da aka ji irin tarin da ta yi a 2021
  • Wannan Baiwar Allah ta nuna hoton asusunta, inda ta yi ikirarin cewa ta tara Naira miliyan biyar
  • A cewar wannan matar, ta tara duka wadannan makudan miliyoyi ne a cikin kasa da shekara guda

Nigeria - Kwanan nan ne aka samu wata mata da labarinta ya ba jama’a mamaki bayan an ji irin ajiyar da tayi a cikin asusun da take tara kudi a gida.

A yayin da kowa yake bayanin irin nasarorin da ya samu a shekarar nan, wannan mata ‘yar Najeriya ta ce ta tara kudi masu yawa cikin asunsunta.

Kamar yadda shafin Pulse Nigeria na Instagram ya nuna, wannan mata ta tara sama da Naira miliyan biyar daga tarin da ta rika yi a asusun na ta.

Kara karanta wannan

Matar aure: Abin da yasa na yi garkuwa da kai na, na nemi miji na ya biya N50,000

Domin tabbatarwa Duniya cewa ba wasa take yi ba, matar ta nuna hoton asusun dankare da miliyoyin kudin da ta ce duk a kwanan nan ta tara su.

'Dirty Decemeber'

A cewar wannan mata da ta bayyana sunan ta a matsayin Geerexxx, a cikin watanni goma kacal, ta iya tara Naira miliyan biyar da duba dari uku (N5.3m).

Da ta ke bayyana farin cikinta a shafinta na Instagram, wannan sabuwar attajira ta nuna ta rika boye kudin da ta samu daga Junairu zuwa watan Oktoba.

Wata mata
An adana N5m a asusu Hoto: Instagram/@pulsenigeria247
Asali: Instagram

Kamar yadda aka saba fito da kudin da aka boye a karshen shekara, wannan mutumiya mai ‘dan karen wayau da adana ta tashi da miliyoyi a Disamba.

Me mutane suke fada a Instagram?

Nan take mutane suka shiga yin lissafin da ba a tambaye su ba, su na neman inkarin ta yadda aka tara wadannan miliyoyin kudi a cikin karamin asusu.

Kara karanta wannan

Jami'ar Soja ta gamu da cizon maciji cikin ban dakin gidanta dake barikin Soji, ta mutu

Masu bibiyar shafukan sada zumuntan da-dama su na ganin ba zai yiwu a sa miliyoyi a asusu ba.

“Mu yi lissafi. Idan za ka samu N5.3m, dole ka samu sinkin N1, 000 har 53… Sai an samu takardun N1000 har 5300 kafin su cika N5.3m. A dai sake duba akwatin nan. - @diplodesmond
“Sannu! Kudin da na ke gani a hoton nan bai kama hanyar N1m ba. Sai dai idan akwai ‘yan Dala 10 ne da idanu ba su gani…” - inji @thefixer__

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng