Yadda Ministan Buhari ya aurar da kyawawan ‘Yan biyunsa mata 2 a rana 1 a Amurka
- An sha biki yayin da karamin Ministan kiwon lafiya, Olorunnimbe Mamora, ya aurar da ‘ya ‘yansa.
- Sanata Olorunnimbe Mamora ya aurar da tagwayensa Oluwadahun Taiwo da Oluwadara Kehinde.
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika jawabi na musamman yayin da aka daura masu auren.
United States - A karshen makon jiya ne aka ji cewa karamin Ministan kiwon lafiya, Olorunnimbe Mamora, ya aurar da tagwayen ‘ya ‘yansa mata a kasar waje.
A ranar Lahadi, 31 ga watan Oktoba, 2021, Sanata Olorunnimbe Mamora ya aurar da ‘ya ‘yan na sa; Oluwadahun Taiwo da Oluwadara Kehinde a kasar Amurka.
Daily Trust tace an yi wannan biki ne a Hyatt Regency O’Hare da ke birnin Chicago a kasar ta Amurka.
An fitar da wasu daga cikin hotunan da aka dauka wajen wannan biki, inda aka ga amaren da angwayensu da sauran ‘yanuwa da abokan arziki ana murna.
Mamora yana cikin manyan ‘yan siyasar Legas, kuma jigo ne a APC. A shekarar 2019 shugaba Muhammadu Buhari ya nada shi karamin Ministan lafiya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sun ce ‘Eh’ a rana daya, aure a rana guda
Jaridar PM News tace Oluwadahun Taiwo da Oluwadara Kehinde sun amince su auri samarinsu; Bayo da Lanre ne a lokaci guda; ranar 10 ga watan Junairu, 2021.
Abin ban sha’awar kuma sai aka ji wadannan Bayin Allah za su shiga daga ciki a rana guda.
An yi nasarar hada auren na su ya fado a lokaci daya ne da taimakon abokai da kuma ‘yanuwa. A yanzu burin kowane daga cikinsu ya tabbata, sun auri masoyansu.
Muhammadu Buhari ya aiko sakon taya murna
Mai girma shugaban Najeriya Muhammadu Buhari bai samu halartar bikin ba, amma ya fitar da jawabi ta bakin hadiminsa, Femi Adesina, yana taya su murna.
“Shugaban kasa Muhammadu Buhari yana taya Dr. Olorunnimbe Mamora murnar auren tagwayen ‘ya ‘yansa, Oluwadahun Taiwo, da Oluwadara Kehinde.”
“A madadina da iyalina, ina so in mika sakon taya murna da addu’o’i na musamman yayin da ‘ya ‘yanka suka dauki wannan layi a rayuwarsu.” – Femi Adesina
Asali: Legit.ng