Latest
Rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta yi nasarar fafatawa da 'yan bindiga. 'Yan sandan sun dakile yunkurin yin garkuwa da mutane da miyagun suka yi.
Gwamnatin Neja na tantance malamai don inganta koyarwa. An karrama tsoffin dalibai kamar Abdulsalami da Sani Bello a taron tsoffin daliban GSS Bida.
Rahotanni sun ce mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara ya kaddamar da gina masallacin Naira miliyan 350 a mahaifarsa da ke karamar hukumar Danja, jihar Katsina.
Jigon jam'iyyar PDP mai adawa a Sokoto, Faruku Fada ya dauki nauyin yara har guda 1,000 domin yi musu kaciya kyauta a jihar saboda tallafawa iyayensu.
Ana fargabar 'yan bindiga sun yi awon gaba da wata sabuwar amarya da kawayenta hudu a jihar Sokoto. An ce 'yan bindigar masu biyayya ne ga Bello Turji.
Fitacciyar jarumar TikTok a Arewacin Najeriya, Murja Ibrahim Kunya ta fitar da bidiyon sabuwar waya kirar iPhone 16 da ta saya. Mutane sun yi mata ca.
Kano ta samu sabon AIG na ‘yan sanda a makon nan. Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwar SP Abdullahi Haruna Kiyawa, mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda.
An samu tashin hankali tsakanin matasa da makiyaya a jihar Gombe. Rikicin wanda ya auku ya jawo sanadiyyar rasa rai yayin da wasu mutane suka jikkata.
Najeriya za ta haɗa kai da Pakistan don bunƙasa noma da samar da horo ga ƙwararru, tare da magance kalubale na tsaron abinci da sauyin yanayi, inji Minista.
Masu zafi
Samu kari