Latest
Ƴan majalisar dokokin jihar Ondo sun taka burki kan shirinsu na dakatar da mataimakin gwamnan jihar, Lucky Aiyedatiwa. Sun cimma hakan ne bayan sun gana da Ganduje.
Hukumar yan sandan farin kaya, DSS, ta tsare Sakataren Watsa Labarai na Jam'iyyar PDP, reshen Jihar Benue, Bemgba Iortyom, kuma kawo yanzu ba a san inda ya ke ba.
Wata dalibar jami’ar Ilorin mai shekaru 20 ta kashe kanta bayan wani saurayi da suka hadu a soshiyal midiya ya damfareta N500,000. Ta sha maganin kwari ne.
Rundunar ƴan sandan jihar Bayelsa ta yi rashin ɗaya daga cikin manyan jami'anta. Mataimakin kwamishinan ƴan sandan jihar ya riga mu gidan gaskiya.
Kwamishinan kuɗi da tsare-tsaren kasafi na jihar Benuwai, Michael Oglegba, ya ce tsohuwar gwamnatin Ortom ta boye wa Alia gaskiyar asusun da jihar ke da su.
Yanzu haka an fara aikin tantance Mista Ola Olukoyede a matsayin sabon shugaban hukumar yaƙi da masu cin hanci da rashawa EFCC a majalisar dattawa.
Masu garkuwa sun yi ajalin wani babban dan kasuwa, Alhaji Samiu Jimoh a shagonsa da ke karamar hukumar Mokwa cikin jihar Neja bayan yi musu tirjiya.
Shugaba Bola Tinubu ya yi wasu nade-nade da su ka jawo cece-kuce a tsakanin al'umma tun bayan hawanshi karagar mulki a watan Mayu na wannan shekara.
Gwamnatin Katsina karkashin jagorancin Malam Dikko Radda ta tabbatar da cewa ba zata yi zaman sulhu da kowane ɗan bindiga ko kungiyar 'yan ta'adda ba.
Masu zafi
Samu kari