Latest
Wani bidiyo dake yawo a soshiyal midiya ya nuno wata matashiyar budurwa tana wawure kudin liki da aka yi wa amarya da ango a wajen bikinsu. Bata san ana kallonta ba.
Daga filayen da aka buga gasar Champions League, Kofin Duniya da manyan wasanni a kasa, Legit ta yi nazarin filayen da za a buga gasar EURO 2024 a Jamus.
Jam'iyyar APC reshen jihar Kano ta buƙaci kowane ɓangare ya martaba yarjejeniyar zaman lafiyan da suka sanya wa hannu a hedkwatar yan sanda makon jiya.
Shugaban majalisar wakilan tarayya, Tajudeen Abbas, ya yi sauye sauye a shugabancin kwamitocin majalisar 26 da ƙarin kwamiti ɗaya a zaman ranar Jumu'a.
Yayin da ake tunkarar bukukuwan kirsimeti, an fara shiga matsalar ƙarancin takardun Naira a wasu sassan jihar Ondo musamman a Akure, babban birnin jihar.
Hatsarin jirgin sojin da ya auku a Patakwal, babban birnin jihar Ribas shi ne na hudu da ya faru a shekarar 2023 wada ke shirin karewa nan da wata ɗaya.
Gwamnan jihar Abia Alex Otti ya sanar da shirin karin mafi karancin albashi ga ma'aikata a jiharsa. Gwamnan zai kuma biyar yan fansho kudaden da suke bin bashi.
Rahoton shelkwarar soji ya nuna cewa dakarun soji sun kashe sama da 'yan ta'adda 180, sun cafke 204 yayin da suka kubutar da mutum 234 da aka yi garkuwa da su.
Dan majalisar tarayya, Alhassan Doguwa, ya karyata ikirarin cewa Shugaban kasa Bola Tinubu ya gabatarwa yan majalisa da fankon kasafin kudin shekara mai zuwa.
Masu zafi
Samu kari