Latest
Wata mata mai shekaru 35 ta yanke jiki ta fadi, ta kuma mutu nan take a sansanin 'yan gudun hijira da ke jihar Benue. Ta mutu ta bar yara shida har da 'yan biyu
Rundunar sojin Najeriya ta gano wurin da 'yan ta'adan ISWAP ke hada burodi a jihar Borno. Sojojin sun lalata wurin tare da sauran kayan hada burodin
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya kai ziyara ta musamman ga dakataccen sanatan Bauchi ta Tsakiya, Abdul Ningi ranar Litinin.
Ministan ilimi, Farfesa Tahir Mamman ya bayyana shirin fara aiwatar da shekaru 18 a matsayin mafi ƙarancin shekarun shiga jami'o'i domin gyara karatun.
Charterhouse Lagos sabuwar makarantar firamare ce da aka kaddamar a Lekki kuma ita ce makaranta mafi tsada a Najeriya a halin yanzu, ana biyan N42m a shekara.
Alkalin babbar kotun jihar Kano, Usman Mallam Na'abba ya warware wani hukunci da kotun da ta yi a baya na dakatar da Abdullahi Ganduje daga jam'iyyar APC.
Rundunar sojojin Najeriya ta bayyana cewa dakarunta da ke aikin wanzar da zaman lafiya a Arewa maso Gabas sun halaka ƴan ta'adda biyu a jihar Borno.
Mai ba shugaban ƙasa shawara kan tsaron ƙasa (NSA), Malam Nuhu Ribaɗu ya bayyana cewa Najeriya za ta bi hanyoyin zama wajen kawar da ta'addanci a ƙasar.
Shugaban kasan Najeriya, Bola Tinubu, ya tabo batun matsalar ta'addanci da hako ma'adanai ba bisa ka'ida da suka zama ruwan dare a nahiyar Afirika.
Masu zafi
Samu kari