
Latest







A ranar Laraba, majalisar dattawa ta gabatar da kudurin hukuncin dauri na watanni 6 ga iyayen da suka yi watsi da ƴaƴansu tare da ƙin tura su makarantar boko.

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya nuna damuwa kan yadda ake samun karuwar masu ba 'yan bindiga bayanaiɓa kauyukan da ke fama da rashin tsaro.

An ayyana kasar Finland a matsayin mafi farin ciki a duniya, yayin da Najeriya ta gaza shiga jerin 20 ɗin farko na jadawalin kasashe masu farin ciki a 2024.

Asirin wata matar aure ya tonu bayan ta yi garkuwa da kanta tare da karbar kudin fansa N2m daga mijinta tare da raba kudin da saurayinta a Abuja.

Mallam Dikko Umaru Radda, gwamnan jihar Katsina, ya ce yin sulhu da 'yan bindiga wata alama ce da ke nuna wa 'yan bindigar cewa sun fi ƙarfin gwamnati.

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi kira da babbar murya ga 'yan majalisu da su bari ministocinsa su yi aikinsu, ta hanyar daina takura musu da yawan kira.

A ranar Laraba ne majalisar wakilai ta amince da sabuwar dokar ƙarin albashi da alawus ga babban joji na ƙasa (CJN) da sauran alƙalan kotunan Najeriya.

Shugaban kasa Bola Tinubu ya haramta wa ministoci da sauran muƙarraban gwamnati tafiye-tafiye zuwa waje. An dauki matakin ne domin rage kashe kudaden jama'a.

Yayin da farin jinin jam'iyyar NNPP ke neman dusashewa a Kano, jigon jam'iyyar, Razaq Adebirigbe ya ce wannan ba sabon abu ba ne a siyasa amma za su yi galaba.
Masu zafi
Samu kari