Bashir Maishadda da zuƙeƙiyar Amaryasa Jaruma Hassana sun Shilla yawon Shaƙatawa
- Sabbin ma'aurata a Kannywood, Abubakar Maishadda, da Amarya Hassana Muhammad Sun tafi dubai hutawa
- Wani bidiyon Amarya da Ango a kan hanyarsu ta tafiya Honeymoon da aka fitar ya ƙayatar da mutane musamman masoya
- A ranar Lahadi, 13 ga watan Maris, aka ɗaura Auren masoyan biyu a masallacin Murtala dake cikin birnin Kano
Fitaccen Furodusa a masana'antar shirya fina-finan Kannywood, Abubakar Bashir Maishadda ya tafi yawon shaƙatawa Honeymoon da Amaryarsa, Hassana Muhammad.
A wani bidiyo da shafin Kannywood Empire ya saki a kafar sada zumunta ta Instagram, sabbin ma'auratan sun nufi Dubai domin shakatawa bayan aure.
A cewar shafin:
"Abubakar Bashir Maishadda tare da amaryarsa Jaruma a Kannywood, Hassana Muhammad, a hanyar zuwa Dubai domin hutawa."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A ranar 13 ga watan Maris, 2022, aka ɗaura auren Babban Furodusan Kannywood, Maishadda tare da Masoyiyarsa Jarumar Fim, Hassana Muhammad.
Auren wanda ya samu halartar ɗaruruwan mutane, an ɗaura shi ne a Masallacin Murtala dake cikin kwaryar birnin Kano.
Auren masoyan dai ya ja hankalim mutane musamman masu bibiyar masana'antar Kannywood kasancewar ba kasafai ake samun aure tsakanin Jarumai ba.
Manyan jaruman Kannywood da suka haɗa da Ali Nuhu, Umar M Sharif, Adam A Zango, da sauran su, sun halarci ɗaura auren domin su shaida.
Bayan daurin auren, Maishadda ya je shafinsa na kafar sada zumunta domin nuna godiya ga Allah, inda ya yi hamdallah tare da neman masoya da su taya su da addu’a.
Ma'auratan sun shirya shagali da dama domin murnar auren su kama daga Dinner da sauran su, sun kuma fitar da Hotuna masu ƙayatarwa.
A wani labarin kuma Tsohon gwamnan Ondo ya faɗi ainihin dalilin da yasaya sake sauya sheka zuwa PDP
Tsohon gwamnan jihar Ondo da ya sauka ya bayyana dalilansa na sake komawa PDP bayan ya barta tun shekarar 2018.
Dakta Olesegun Mimiko ya ce ya dawo PDP ne domin sake fasalinta da kuma shirya kwato mulki daga hannun APC.
Asali: Legit.ng