Sabbin bidiyoyin Maishadda da Hassana suna rungumar juna kafin aure sun janyo cece-kuce
- Bayyanar sabbin bidiyoyin Furodusa Maishadda da amaryarsa Hassana suna rungumar juna ya janyo cece-kuce
- A sabbin bidiyoyin, an gansu suna daukar hotunan kafin aure inda angon ke cukuikuyar amaryar duka da ba a daura auren ba
- Tuni wasu daga cikin masoyansu suka dinga nuna sun birge su yayin da wasu suka dinga tsokacin Allah wadai kan wannan dabi'a
Wasu bidiyoyi da ake ta yadawa na Furodusa Abubakar Bashir Maishadda tare da amaryarsa Hassana inda aka gansu suna rungumar juna yayin daukar hotunan kafin biki sun janyo cece-kuce.
Wasu daga cikin masoyansu sun dinga yaba musu yayin da wasu kuwa suka dinga tofin Allah wadai da Allah ya shirya kan lamarin ganin cewa ba daura auren aka yi ba.
Wasu sun danganta hakan da yanayin rayuwar 'yan fim da kuma wata irin sabuwar rayuwar wayewa da ta samu jama'a.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Martanin jama'a kan bidiyon
Bayyanar bidiyon ke da wuya, jama'a suka fara yin martani tare da cece-kuce a kai
Abdullah Yakasai ya ce: "Masu koya Tarbiyya a kasar Hausa kenan..."
Auwalu Shehu Wudi ya ce: "Sai fa an yi auren ya dace a yi wannan tsarin. Amman gaskiya babu kyautawa a nan. Allah ya shirya ku."
Musa Adamu tsokaci yayi da: "Sun karyata Sarkin Waka. To maganar shi ta fito Fili. Allah ka shirya mana jama'ar Musulmai Amin."
Muhammad Abdullahi Aliyu cewa yayi: "Hasbunallahu Wani'imal Wakil. Ya Allah ka kara kare mana imaninmu. Wai yanzu wannan idan aka ce ta yankashi mutane su ringa mamaki. Wannan duk abinda ta mar na rashin da'a da wulakanta iyayensa ba zan yi mamaki ba. Ya Allah ka nesanta mu da hada zuriyya da irin wannan mutanen. Ga kauyanci ya zagaye mutum amma gani yake shi wayayye ne. Allah ya shirya."
Martanin Ango Maishadda
Sai dai alamu sun nuna ba a son ran furodusa Maishadda aka saki bidiyon ba ko kuma bai ma san ana dauka ba sai dai ganin su yayi suna yawo a kafar sada zumuntar zamani.
Bayan wannan bidiyon ya karade kafafen sada zumunta, Furodusa Maishadda ya yi wani rubutu a shafinsa na Instagram inda yake neman yafiyar Ubangiji tare da neman tsari daga masu shirya masa kutunguila.
Ya rubuta:
"Ya Rabbi ka sa mu cika da kyau da imani. Ya Rabbi ka kare mu daga dukkanin kutunguila da sharrin makiyanmu na fili da na boye albarkacin sirrin Fatiha. Ameen summa Ameen."
Asali: Legit.ng