Labaran duniya
Wani jirgin sama dauke da mataimakin shugaban kasar Malawi, Saulos Klaus Chilima da wasu mutane tara ya bace, kamar yadda fadar shugaban kasar ta sanar.
Babban ministan Isra'ila, Benny Gantz ya ajiye aiki bayan sabani da ya samu da firaminista Benjamin Netanyahu kan rikicin da ake tsakanin Isra'ila da Falasdinawa.
Biyo bayan yawaitar mutuwar mahajjata a kasar Saudiyya saboda tsananin zafi, an dauki matakan sanyaya yanayi domin rage mutuwar mutane yayin aikin hajji.
Hukumomi a kasar Saudiyya sun tabbatar da cewa wata mata mai suna Hajiya Hawawu daga Kwara ta rasu, binciken da aka gudanar ya tabbatar da cewa ta yi ajalin kanta.
Babu wata hukumar gwamnati da ke iya dokance hada-hadar kudi a kasuwar Crypto. A wannan rahoto, mun tattara muhimman bayanai game da amfani da illolin Crypto.
Yayin da Kungiyar Kwadago ta NLC ke takun-saka da gwamnatin Najeriya, mun kawo muku rahoton kasashen Afirka da suka fi biyan mafi karancin albashin ma'aikata.
Tsohon Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani ya yaba da yadda 'yan majalisar jiharsa suka bankado zargin badakala a gwamnatin Nasir El Rufa'i.
Jami'an tsaro na musamman sun kama gungun yan damafara masu cutar mutane da sunan sama musu izinin aikin Hajji a Makka. An kama su da abubuwa da dama.
Hukumomi a kasar Saudiyya sun tabbatar da ganin watan Dhul Hijjah a yammacin yau Alhamis 6 ga watan Yuni inda aka tabbatar da gobe 1 ga watan Dhul Hijjah.
Labaran duniya
Samu kari