Labaran duniya
Wata kotu dake zamanta a Koriya ta kudu ta umarci shugaban rukunin kamfanonin SK, Chey Tae-won ya biya tsohuwar matarsa Roh So-young won tiriliyan 1.38.
Wata kotu dake zamanta a Manhattan dake Amurka ta kama tsohon shugaban kasar, Donald Trump da manya-manyan laifkua 34, ciki har da bayar da kudin toshiyar baki.
Firaministan Birtaniya, Rishi Sunak ya yi magana kan cewa a yau ba sai mutum ya mallaki digiri zai yi nasara ba. Mutane na mayar masa da martani daga fadin duniya.
Wata maniyyaciya daga jihar Kebbi ta rasu a birnin Makka da ke kasar Saudiyya a ranar Asabar 25 ga watan Mayu bayan ta sha fama da gajeruwar jinya na wani lokaci.
Kamfanin Tapswap ya magantu yayin da yan Najeriya ke samun cikas a kokarin neman kudi ta hanyar dangwale bayan sun gagara shiga manhajar a kwanakin nan.
An yi amfani da gurbattacen jini a Birtaniya na tsawon shekaru wanda ya jawo mutuwar mutane da dama da kuma yaduwar cututtukan kanjamau da ciwon hanta.
Yayin da ake jimamin mutuwar shugaban kasar Iran, Ebrahim Raisi, Amurka ta nuna damuwa kan yadda marigayin ya bar duniya da alhakin mutane da dama.
Shugaban kasar Iran, Ebrahim Raisi ya rasa ransa a wani hatsarin jirgin sama. Ya zama shugaban kasa na 15 da ya rasu sakamakon hatsarin jirgin sama.
A yayin da ake zaman makokin mutuwar shugaban kasar Iran, Ebrahim Raisi, an ruwaito cewa girgizar kasa mai karfin 3.7m ta afku a yammacin kasar Iran a yau Litinin.
Labaran duniya
Samu kari