Trump Ya Tsokano Fada, Macron Ya Yi Masa Zazzafan Martani

Trump Ya Tsokano Fada, Macron Ya Yi Masa Zazzafan Martani

  • Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron, ya fuskanci kalaman ba'a daga wajen takwaransa na Amurka, Donald Trump
  • Emmanuel Macron ya tsinci kansa Trump na yi masa kalaman ba'a dangane da aurensa inda ya nuna cewa yana shan wahalar matarsa
  • Sai dai, shugaban kasar na Faransa ya tanka kan kalaman da Trump dangane da aurensa da Brigitte Macron

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Seoul, Koriya ta Kudu - Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, ya yi martani kan kalaman ba'a da shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi masa dangane da aurensa.

Emmanuel Macron ya bayyana cewa kalaman ba'a da Donald Trump ya yi game da aurensa ba su cancanci mayar da martani ba.

Macron ya yi wa Donald Trump martani
Shugaba Donald Trump da Emmanuel Macron na Faransa Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Tashar RTE ta ce Emmanuel Macron ya bayyana hakan ne yayin da yake tattaunawa da manema labarai yayin wata ziyara a birnin Seoul na kasar Koriya ta Kudu.

Kara karanta wannan

Bayan haura wata 1 ana yaki, Shugaba Macron ya fada wa Amurka gaskiya kan shirin nukiliyar Iran

Shugaban na Faransa ya kira kalaman na Trump a matsayin waɗanda "ba su dace ba kuma ba su kai matsayin da ya kamata ba."

Bayan kwanaki ana takun-saka kan hare-haren Amurka da Isra'ila a Iran da kuma batun ƙungiyar NATO, Macron, wanda ya nuna bacin ransa, ya soki salon mulkin Trump inda ya ce "surutu ya yi yawa" kuma "wannan ba wasan kwaikwayo ba ne."

Trump ya yi ba'a ga Emmanuel Macron

A ranar Laraba, Trump ya yi ba'a ga shugaban na Faransa da matarsa a wani taron cin abinci na sirri, yayin da yake sukan ƙawayen NATO kan rashin shiga yaƙi da Iran.

Shugaban na Amurka ya kwaikwayi muryar mutanen Faransa, yana mai cewa matar Macron "tana wulaƙanta shi sosai" kuma har yanzu Macron yana "ƙoƙarin farfaɗowa daga naushin da aka kai masa a kumatu."

Wani martani Macron ya yi wa Tinubu?

Yayin ziyarar a birnin Seoul na ƙasar Koriya ta Kudu, inda yake tare da matarsa Brigitte, Macron ya ce kalaman Trump "ba su da kyan ji kuma ba su dace da matsayin shugabanci ba.", tashar NDTV ta kawo rahoton.

Kara karanta wannan

Rashin taya Trump yaki da Iran ya harzuƙa shi, ya ci mutuncin Shugaban Faransa da matarsa

"Don haka ba zan mayar musu da martani ba, ba su cancanci hakan ba."

- Emmanuel Macron

Macron ya yi wa Trump martani
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump Hoto: Andrew Caballero-Reynolds
Source: Getty Images

Macron ya ce ya kamata a mayar da hankali wajen "yin aiki don kwantar da tarzoma" a Gabas ta Tsakiya da kuma cimma yarjejeniyar tsagaita wuta.

Shugaban na Faransa ya nuna damuwa kan yadda yadda Trump yake yawan sauya manufofinsa kan yakin lokaci zuwa lokaci. "Akwai surutu da yawa, kuma maganganun a hargitse suke."

"Dukkanmu muna buƙatar daidaito, natsuwa, da komawa ga zaman lafiya wannan ba wasan kwaikwayo ba ne!"

- Emmanuel Macron

Alkali ya kawo matsala ga Trump

A wani labarin kuma, kun ji cewa kotu ta kawo cikas ga shugaban kasar Amurka, Donald Trump kan shirin da yake yi na gina katafaren dakin taro.

alƙalin kotun tarayya a Amurka ya dakatar da Shugaba Donald Trump daga ci gaba da kowane irin aiki kan katafaren zauren taro na dala miliyan 400 da ake shirin gina wa.

Mai shari'a Richard Leon, ya bayyana cewa shugaban Amurka amintaccen mai kula da fadar ne kawai, amma ba shi ne mamallakin gidan ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng