Wata Sabuwa: Gagarumar Matsala Ta Tunkaro Isra'ila ana Tsaka da Yaki da Iran

Wata Sabuwa: Gagarumar Matsala Ta Tunkaro Isra'ila ana Tsaka da Yaki da Iran

  • Ana ci gaba da ba hammata iska a yakin da ake yi a tsakanin Amurka, Isra'ila da Iran a yankin Gabas ta Tsakiya
  • Yayin da ake ci gaba da yakin, wata sabuwar matsala ta tunkaro rundunar sojojin Isra'ila
  • Wasu daga cikin sojojin sun fara bijirewa bayan sun dade suna fadin bukatunsu, ba tare an share musu hawaye ba

​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Tel- Aviv, Isra'ila - Jami'an rundunar sojojin Isra'ila (IDF) da dama sun ki zuwa wuraren aikinsu.

Sojojin rundunar IDF sun ki zuwa wuraren aikinsu saboda karancin kayayyakin kariya daga makaman roka da makamai masu linzami.

Sojojin Isra'ila sun fara kin zuwa wurin aiki
Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu Hoto: Abir Sultaan
Source: Getty Images

Jaridar Jerusalem Post ta kawo rahoton a ranar Laraba, 18 ga watan Maris 2026.

Meyasa sojojin ba su zuwa wajen aiki?

Sojojin, waɗanda ɓangare ne na rukunin masu sa-kai, sun yi iƙirarin cewa sun kwashe tsawon wata guda suna gabatar da wannan matsalar ga rundunar IDF, amma ba a ɗauki kowane mataki don magance ta ba.

Kara karanta wannan

Iran ta samu nasara, sababbin makamanta sun yi gagarumar barna a Isra'ila

Sojojin sa-kan sun buƙaci shugabanninsu da su samar musu da mafaka a sansaninsu sau da dama, amma ana ƙin amincewa, wani lokacin ma har da watsi da batun gaba ɗaya, wasu lokutan kuma ana kafa hujja da matsalolin kai-da-kawowa.

A wani lokaci, an gaya wa sojojin cewa "ana kan hanyar kawo mafaka" amma an soke isar da ita bayan iƙirarin cewa hanyar da za ta kai sansanin ba ta biyuwa.

Sojojin Isra'la sun harzuka

Wani soja ya bayyana cewa:

"Wannan babban sakaci ne, abin tsoro ne, kuma yana da haɗari. Lokacin da aka kuwwar ƙarar gargaɗin harin sama ta tashi, sai dai mu sanya hular mu yi addu'a. Wannan abin kunya ne. Me za su gaya mana idan soja ya ji rauni? Shin za su ce 'za mu ɗauki darasi ne'?"
"Yayin da ƙasar nan ke ci gaba da jaddada wa ‘yan ƙasarta muhimmancin shiga wuraren kariya daga bama-bamai, ita kanta rundunar sojojin tana tura sojoji zuwa sansanoni ba tare da wata mafita ba."

Matsalar rashin isashshiyar kariya a sansanonin IDF ta zama ruwan dare, inda ake samun rahotanni da dama na larancin mafaka a faɗin ƙasar duk da sananniyar barazanar rokoki da makamai masu linzami da ake fuskanta a lokacin wannan farmaki na Operation Roaring Lion.

Kara karanta wannan

Sojoji sun fara neman sauran ƴan ƙunar baƙin wake a Borno, an nemi daukin jama'a

"Rundunar IDF, wadda ke kakkabo makamani masu linzami tare da dakile 'yan ta'adda daga nisan kilomita 2,000, ta kasa kai mafaka zuwa sansaninmu don ceton rayuka?"

- Wani soja

Sojojin sun Isra'ila sun fara kin zuwa wurin aiki
Wasu dakarun sojojin Isra'ila Hoto: Anadolu
Source: Getty Images

Me rundunar IDF ta ce kan lamarin?

A matsayin martani ga waɗannan zarge-zargen, rundunar IDF ta bayyana cewa tana shirya wani babban tsari na kare dakarunta, dangane da nazarin yanayi da kuma gaggawar da aikin ke buƙata.

Rundunar IDF ta bayyana cewa:

"A lokacin fafatawa, an riga an tura ƙarin matakan kariya zuwa sansanoni da rukunoni daban-daban."
"An horar da dukkan sojoji yadda za su zauna na tsawon lokaci, suna bin ƙa'idar neman 'wuri mafi kariya da za a iya samu'."

Isra'ila ta kashe Minista a Iran

A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar sojojin Isra'ila ta sake kashe wani babban jami'i a gwamnatin Iran.

Rundunar IDF ta bayyana cewa ta hallaka Ministan leken asirin Iran, Esmaeil Khatib, a wani hari da aka kai masa a birnin Tehran.

Kisan Esmaeil Khatib na zuwa ne bayan Isra'ila ta kashe shugaban majalisar tsaron Iran, Ali Larijani da babban kwamandan dakarun Basij, Gholamreza Soleimani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng