Yadda Amurka da Isra'ila ke amfani da AI wajen bin diddigi da kai hari kan mutane

Yadda Amurka da Isra'ila ke amfani da AI wajen bin diddigi da kai hari kan mutane

A halin yanzu, kirkirarriyar basirar AI ta zama ginshiki a yakin zamani, inda take sauya yadda ake tsara hari da kuma aiwatar da shi. Kasashen Amurka da Isra’ila na amfani da wadannan na’urorin AI wajen gano wuraren hari, tattara bayanan sirri, da kuma daidaita hare-haren soji yadda suke so.

Duk da cewa wadannan na’urori na samar da saurin aiki da kwarewa wajen isar da aikin, suna kuma tada gagarumar alamar tambaya game da batun da’a, musamman wajen fayyace tsakanin sojoji da farar hula, da kuma ikon yanke hukuncin rayuwa da mutuwa ga na’ura.

Yadda Isra'ila ke amfani da AI wajen yaki
Isra'ila da Amurka na amfani da AI a yakinsu | Hoto: Anadolu/x
Source: Getty Images

Ga jerin wasu daga cikin muhimman na’urorin da Amurka da Isra’ila ke amfani da su:

Bi-diddigin wayoyin salula

Sojojin Isra’ila na amfani da wata fasahar AI da ke bibiyar inda wayoyin salula suke a fannin tsaro da yake-yake da suke yi.

Wannan tsarin yana sanya ido kan yadda Falasdinawa ke kaurace wa yankin Arewacin Gaza, wanda hakan ke taimaka wa sojoji sanin motsin jama’a yayin ci gaba da mamaye Zirin Gaza.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta tsoma baki a rigimar Iran da Isra'ila, Najeriya ta ba da shawara

Fasahar "The Gospel"

"The Gospel" wata na’ura ce ta Isra’ila da ke fitar da jerin gine-gine ko wasu wurare da ya kamata a kai wa hari.

Tana gudanar da aikin gano wuraren hari ne kai tsaye ba tare da jiran dan Adam ba, lamarin da ke barazana ga tsaron farar hula a Zirin Gaza da sauran wuraren harin Isra’ila.

Fasahar "Lavender"

Ita kuma "Lavender" tana amfani da bayanai ne wajen sanya wa mutane maki a Gaza, dangane da zargin alakar su da kungiyoyin mayakan Falasdinawa.

Isra’ila na amfani da wadannan maki wajen ayyana mutum a matsayin wanda za a iya kai wa hari kuma tsari ne da ake suka saboda fargabar kuskure wajen harbin farar hula.

Fasahar "Where’s Daddy?" (Ina Baba?)

Sojojin Isra’ila na amfani da wani tsari mai suna "Where’s Daddy?", wanda aka kera don tantance lokacin da wanda ake nema ya isa wani takamaiman wuri domin a kai masa hari a can.

Kara karanta wannan

Babban jami'in gwamnatin Amurka zai dura a Najeriya kan batun ta'addanci

Wannan na’urar tana mayar da hankali ne wajen sanin daidai lokacin da mutum yake a gida ko wani wuri muhimmi kafin kai masa hari.

Yarjejeniyar OpenAI da Ma'aikatar Tsaron Amurka (Pentagon)

A ranar 28 ga Fabrairu, shugaban kamfanin OpenAI, Sam Altman, ya tabbatar da kulla yarjejeniya da Ma’aikatar Tsaron Amurka bayan da tsohon dan kwangilar ma’aikatar, wato kamfanin Anthropic, ya nuna damuwa kan batun da’a.

Yadda Amurka da Isra'ila ke amfani da AI a yaki
AI na taimakawa Isra'ila da Amurka a yaki | Hoto: Nathan Howard - Pool, Mahsa / Middle East Images / AFP.
Source: Getty Images

Altman ya bayyana cewa Pentagon ta amince cewa ba za a yi amfani da fasahar OpenAI wajen "leken asirin jama'a a cikin gida" ko "kera makaman da ke harbi da kansu ba," yana mai jaddada cewa mutane ne za su dauki "alhakin amfani da karfin soja."

Amfani da Anthropic AI a Harin Amurka kan Iran

A ranar 1 ga Maris, kafar yada labarai ta NDTV ta bayar da rahoton cewa gwamnatin Amurka ta yi amfani da na’urorin Anthropic AI yayin wasu hare-hare da ta kai a Iran.

Rundunar sojin Amurka ta tsakiya ta yi amfani da na’urorin wajen tantance bayanan sirri, gano wuraren hari, da kuma gwada yadda yakin zai kasance kafin a fara shi.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun saka harajin yin wa'azi a watan Ramadan

Wannan ya faru ne sa’o’i kadan bayan Shugaba Donald Trump ya ba da umarnin cewa hukumomin gwamnatin tarayya su daina amfani da fasahar Anthropic.

Amfani da AI a fagen yaki da Isra'ila da Amurka ke yi na nuni da yadda fasaha ke sauya dabarun soji a fannin farmaki da kare kai.

Kamfanin Anthropic na shirin kalubalantar matakin gwamnatin Trump na sanya shi a matsayin "barazana ga tsaron kayayyakin bukatu" a gaban kotu.

Hakan ya zama daya daga cikin kalilan din kamfanonin da suka tunkari manufofin shugaban Amurka a wa’adinsa na biyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and leads the Hausa Desk at Legit.ng. He is AfricaCheck's ambassador and HumAngle Technology and Civic Impact Fellow. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. His commitment to excellence has earned him recognition, including the Legit Fearless Team Player of the Year 2023 and 2024 Distinguished Editorial Leadership Award. Email: salisu.ibrahim@corp.legit.ng