Wani Mutum Ya Maka Lauyan Mutum-Mutimi Na Farko Kotu Kan Shiga Aikin Shari'a Ba Bisa Ka'ida Ba
- An maka lauya mutum-mutimi na farko a gaban wata kotu da ke Amurka saboda shiga aikin ba da lasisi ba
- An zargi lauya mutum-mutimin da karya dokokin birnin kalifoniya na yi ayyukan shari'a marasa sahihanci
- Mai ƙarar ya nema a dakatar da mutum-mutimin sannan a ayyana cewa shi ba lauya ba ne
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Amurka - An shigar da ƙarar lauya mutum-mutimi na farko mai suna 'DoNotPay' a gaban ƙuliya a ƙasar Amurka, saboda shiga harkokin shari'a ba tare da lasisi ba.
An dai gina shi wannan lauya na mutum-mutimi ne bisa doron sabuwar fasahar nan ta AI, kamar yadda shafin Lawyers Weekly ya wallafa.
Lauyan na mutum-mutimi ya kasance yana taimakawa jama'a wajen harkokin da suka shafi shari'a.
Lauyan na mutum-mutimi na gudanar da ayyukan shari'a ba tare da lasisi ba
Wanda ya shigar da ƙara, Jonathan Faridian ya ce lauyan na mutum-mutimi na gudanar da ayyuka na shari'a marasa inganci kuma ba bisa ƙa'ida ba, wanda hakan ya saɓawa dokokin aikin na birnin Kalifoniya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ƙara da cewa mutum-mutimin ba shi da digiri a ɓangaren shari'a, kuma ba shi da wata cibiya ta shari'a.
Haka nan ya ce ba a rantsar da shi a wata hukuma ta lauyoyi ba, kuma babu wani lauya da yake lura da shi don sanya shi a hanya.
Ayyukan da ake zargin lauyan na mutum-mutimi na yi ba bisa ƙa'ida ba
Daga cikin ayyukan shari'a da ake zargin mutum-mutimin lauyan da yi akwai shirya yarjejeniyar raba aure tsakanin ma'aurata.
Haka nan an zargi mutum-mutimin lauyan da shiga ƙananun shari'a irin na neman haƙƙi ga mutane, da makamantansu.
Mai ƙarar ya ƙara da cewa lauyan na 'DoNotPay', ba komai ba ne face fasahar AI ta yanar gizo da ke bayar da bayanai na shari'a marasa inganci da mutane suka zuba masa.
Wanda ya ƙirƙiro lauyan na mutum-mutimi Joshua Browder ya bayyana cewa ƙarar da aka shigar ba ta dace ba, kuma zai ƙalubalanceta a kotu, kamar yadda shafin Legal Cheek ya wallafa.
Matashi ɗan asalin Kano da ya ƙera mutum-mutimi ya samu tallafin karatu
Legit.ng a kwanakin baya ta kawo muku rahoto kan wani matashi, Isah Barde, ɗan asalin jihar Kano wanda ya ƙera mutum-mutimi mai motsi, da ya samu tallafin karatu daga NITDA.
Matashin ya ƙera mutum-mutimin mai motsi ne ta hanyar amfani da kwali.
Asali: Legit.ng