Zanga-Zanga Ya Barke A Yayin Da Jami'an Najeriya Da Ke Aikin Kwaso Mutane 'Suka Tsere Daga Sudan'

Zanga-Zanga Ya Barke A Yayin Da Jami'an Najeriya Da Ke Aikin Kwaso Mutane 'Suka Tsere Daga Sudan'

  • Yan Najeriya wadanda suka makale a kasar Sudan biyo bayan barkewar rikici sun yi zanga-zanga
  • Rahotanni sun nuna cewa watsi da su da jami'an da ya kamata su kwaso su zuwa Egypt ne yasa suka yi zanga-zangar
  • Ba a samu ji ta bakin hukumar NiDCOM ba amma majiya daga NEMA ta ce ba zai yi wu jami'an su tsere ba don shugaban NEMA na can yana saka ido

Sudan - Makoman yan Najeriya da suka makale a Sudan na cikin mawuyacin hali sakamakon rashin jituwa da aka samu yayin aikin kwaso su.

Wani majiya da ke da masaniya kan lamarin ya fada wa Daily Trust cewa jami'an ofishin jakadancin Najeriya sun koma wurin iyalansu a Cairo, Egypt sunyi watsi da mutanen da aka shirya kwasowa.

Yan Najeriya a Sudan
Zanga-zanga ya barke a Sudan bayan jami'an Najeriya da ke aikin kwaso mutane 'sun tsere' sun bar su. Hoto: Nigerian Tribune
Asali: Facebook

Sakamakon hana jirage tashi da sauka a Sudan, jiragen da ya kamata su dakko mutane daga Sudan suna da sauka a Egypt da wasu kasashe da ke makwabtaka.

Kara karanta wannan

Da na kowa ne: Wata kasa ta kwaso 'yan Najeriya daga Sudan don kare su daga hadari

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta yi shirin kwashe yan Najeriya da ke Sudan a mota zuwa Cairo kafin daga nan su shiga jirgi zuwa Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An fara aikin kwaso mutanen ne bayan bangarorin biyu da ke rikici sun yarda su tsagaita wuta na kwana uku a Sudan din.

Legit.ng ta rahoto yadda wasu yan Najeriya suka samu matsala a hanyar zuwa Cairo, amma daga bisani an warware matsalar bayan manyan jami'an gwamnati sun shiga tsakani.

Amma, bangarorin biyu da ke yaki a Sudan sun tsawaita tsagaita wutar da kwana uku daga ranar Juma'a.

Sanadin zanga-zangan da yan Najeriya suka yi a Sudan

Sai dai aikin kwaso mutanen ya tsaya saboda jami'an sun tsere daga Sudan kamar yadda aka rahoto.

Hakan ya yi sanadin yin zanga-zanga a wurin da ake kwashe mutane a Khartoum.

Masu zanga-zangar sun rike wani Ibrahim Abdullah, mai sana'ar canjin kudi, suka lakada masa duka.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tarayya Ta Kashe Naira Miliyan 560 Wajen Ceto ‘Yan Najeriya a Kasar Sudan

Baya ga karban kudin da ya kamata a yi amfani da shi domin tafiyar, an ce Abdullah na cikin wadanda aka dora wa alhakin samo motoccin bas.

A cikin faya-fayan bidiyo da murya da Daily Trust ta samu, an jiyo Abdullah na cewa $250,000 da aka fara turo masa ya kare.

Ya ce ba a riga an turo cikon kudin ba, yana cewa kimanin bas 25 da ya kamata su kwaso yan Najeriya sun janye saboda jami'an ba su basu hadin kai.

A ranar Laraba, Abike Dabiri-Erewa, shugaban hukumar yan Najeriya mazauna kasashen waje, NiDCOM ta ce akwai yan Najeriya a kala miliyan uku a Sudan amma Gwamnatin Tarayya ta ce za ta kwashe iya wadda za ta iya.

Dabiri-Erewa ba ta bada amsa dangane da tambayan baya-bayan nan ba game da halin da ake ciki a Sudan domin ba ta daga waya ba kuma ba ta amsa sakon text ba.

Kara karanta wannan

Motocin Da Za Su Kwashe Yan Najeriya a Sudan Sun Isa Garesu a Bidiyo

Mai magana da yawun NiDCOM, Gabriel Odu, ya ce ba shi da ikon cewa komai kan batun a yayin da wakilin majiyar Legit.ng Hausa ya tuntubi Ma'aikatar Kasashen Waje ko NEMA don ji ta bakinsu.

Ba zai yi wu jami'an gwamnati su tsere su bar mutane a Sudan ba - Majiya

Amma babban jami'in NEMA wanda ba ya son a bayyana sunansa don ba a bashi ikon magana kan batun ba ya ce ba zai yi wu jami'an Najeriya su bar yan kasar ba.

Majiyar ta ce:

"Shugaban NEMA na can don sa ido kan kwashe mutanen. Don haka ba zai yi wu ma'aikatan da ke aiki karkashinsa su tsere ba idan shi yana nan."

Motoci Sun Dira Sudan Don Kwaso Daliban Najeriya

Tunda farko kun ji cewa Hukumar kula da yan Najeriya mazauna kasashen ketare, NiDCOM ta ce motocci sun dira kasar Sudan don jigilar yan Najeriya.

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: Bayan Shekaru 8 Da Aure Tare Da Yara 2, Ma’aurata Sun Gano Su Din Yan’uwa Ne, Bidiyon Ya Yadu

Sanarwar da NiDCOM ta fitar ta ce za a kwashe daliban ne zuwa Masar daga nan kuma jirgin sama zai dakko su zuwa gida Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164