Yanzu-Yanzu: Dalibai 'Yan Najeriya Sun Shiga Tsaka Mai Wuya Kan Hanyar Su Ta Dawowa

Yanzu-Yanzu: Dalibai 'Yan Najeriya Sun Shiga Tsaka Mai Wuya Kan Hanyar Su Ta Dawowa

  • Ƴan Najeriyar da aka kwaso daga Sudan domin kai su ƙasar Masar, sun koka kan halin da suka samu kan su a ciki
  • Motocin da su ke ɗauke da su, sun tsaya a tsakiyar hamada kan rashin biyan su haƙƙoƙin su da ba ayi ba
  • Ɗaliban sun galabaita sosai inda suka yi kiran da a taimaka a kawo musu agajin gaggawa domin fita daga ƙuncin da suke ciki

Sudan - Wasu daga cikin ɗalibai ƴan Najeriya da aka kwaso daga rikicin Sudan, yanzu haka sun maƙale a cikin tsakiyar hamada, rahoton Daily Trust ya tabbatar.

Bayan tsagaita wuta da ɓangarorin da ke faɗa da juna suka sanar na kwana uku, ƙasashe da dama sun matsa ƙaimi domin kwashe ƴan ƙasar su daga Sudan.

Yan Najeriya sun shiga tasku akan hanyar dawowa dagaa Sudan
Motocin kwaso 'yan Najeriya daga Sudan Hoto: Vanguard.com
Asali: UGC

A ranar Laraba, gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta fitar da N150m domin ɗaukar hayar manyan motoci 40, da za su kwaso wasu ƴan Najeriya daga Sudan zuwa birnin Alkhahira na ƙasar Masar, inda daga nan za a kwaso su a jirgi zuwa Najeriya.

Kara karanta wannan

Gaskiya Ta Bayyana Kan Dalilin Da Ya Sanya Shugaba Buhari Ya kasa Cika Wasu Alkawuran Da Ya Yi Wa 'Yan Najeriya

Sai dai wasu daga cikin ɗaliban da aka kwaso domin kai su wajen tsiria, sun bayyana halin ƙuncin da suke ciki a tafiyar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wata ɗaliba wacce lamarin ya ritsa da ita wacce ba ta ambaci sunan ta ba, tace direbobin sun sha alwashin ƙin cigaba da tafiyar saboda ba a biya su kuɗin su ba.

A kalamanta:

"Kafin mu fara wannan tafiyar, mun ga abubuwa iri-iri. Saboda Allah mun kwashe sama da sa'o'i biyar muna cikin hamada. Ba mu san halin ma da mu ke ciki ba a yanzu."
"Ba mu da ruwa. Kuɗaɗen mu sun ƙare. Direbobin sun ce ba za su tafi da motocin su ba tunda ba a biya su kuɗin su ba. Ga mu nan maƙale a cikin hamada. Ba mu da komai. Ba ma mu san a inda mu ke ba. Muna cikin wajen da ba mu san ko ina ne ba sannan cikin babban haɗari."

Kara karanta wannan

'Yan Ta'addan ISWAP Sun Lallaba Cikin Dare Sun Sace Ma'aikata Da Jami'an Tsaro a Jihar Borno

Motocin sun cigaba da tafiya

Sai dai a shugabar hukumar kula da ƴan Najeriya mazauna ƙasashen waje, Abike Dabiri-Erewa, ta tabbatar da cewa motocin sun cigaba da tafiyar su yanzu haka.

Abike ta bayyana hakan ne a wani rubuto da ta yi a shafin ta na Twitter, inda ta bayyana cewa shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA), ya tabbatar mata da an shawo kan matsalar.

Gwamnatin Tarayya Ta Sauya Tunani Kan Shirin Cire Tallafin Man Fetur

A wani rahoton na daban kuma, gwamnatin Najeriya ta yi amai ta lashe kan shirin ta na cire tallafin kuɗin man fetur.

Gwamnatin tarayyar ta dakatar da cire tallafin man fetur ɗin wanda aka daɗe ana taƙaddama a kai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

iiq_pixel