Najeriya Ta Shiga Jerin Kasashe 100 Mafi Farin Ciki A Duniya, Duba Sabon Matsayinta
- Yanzu Najeriya ta na a matsayin kasa ta 95 a jerin kasashen da su ka fi farin ciki a duniya a 2023
- A karo na shida a jere, Finland na cigaba da kasancewa ta daya yayin da Denmark da Iceland ke biye ma ta
- Afghanistan ce ke rike da kambun kasa mafi rashin farin ciki a duniya
An bayyana Najeriya a matsayin kasa ta 95 mafi farin ciki a duniya a shekarar 2023, in da ta wuce kasashe 23 daga matakin da ta ke na 118 a shekarar 2022.
Wannan na kunshe ne cikin rahoton farin ciki na duniya da aka fitar ranar Litinin, 20 ga watan Maris, 2023, da Sustainable Development Solutions Network ta fitar.
Abin burgewa, a 2021, Najeriya ce ta 59 a jerin kasashen da suka fi farin ciki, kuma ta biyu a Afirka, a bayan Mauritius.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Rahoton wanda ake tattarawa daga bayanan yadda mutane ke farin ciki, da kuma bayanan jindadi da tattalin arziki na ranar farin ciki ta majalisar dinkin duniya da ake gudanarwa ranar 20 ga watan Maris.
Ana duba manyan abubuwa shida: yanayin farin ciki, shigowar kudi, lafiya, yanci, kyauta, da rashin rashawa.
Ana bada maki daga 0 zuwa 10, tsahon wa'adin shekara uku na farin cikin da ake ciki.
Yadda kasashe ke sauya matsayi a jadawalin
Rahoton ya bayyana Finland a matsayin kasa mafi farin ciki, matsayin da ta ke rike da shi tsahon shekara shida a jere da tazara tsakaninta da sauran kasashe.
Denmark da Iceland ne ke rike da kambun na biyu da na uku. Israel, da ta tsallake kasa biyar daga matakin ta 9 a 2021 yanzu ita ce ta hudu.
Netherlands, Sweden, Norway da Switzerland kowacce na rike da matakin na 5, 6, 7, da 8 a sabon jadawalin. Luxembourg da New Zealand ke biye mu su a matsayin na 9 da 10 don kammala jerin goman farko na kasashe mafiya farin ciki a duniya.
Kasashe mafi murna a duniya a 2023
Lamba | Kasa | Matsakaicin Ƙimar Rayuwa |
1 | Finland | 7.80 |
2 | Denmark | 7.56 |
3 | Iceland | 7.53 |
4 | Israel | 7.47 |
5 | Netherlands | 7.40 |
6 | Sweden | 7.39 |
7 | Norway | 7.31 |
8 | Switzerland | 7.24 |
9 | Luxemborg | 7.22 |
10 | New Zealand | 7.12 |
11 | Austria | 7.09 |
12 | Australia | 7.09 |
13 | Canada | 6.96 |
14 | Ireland | 6.91 |
15 | United States of America | 6.89 |
16 | Germany | 6.89 |
17 | Belgium | 6.85 |
18 | Czech Republic | 6.84 |
19 | United Kingdom | 6.79 |
20 | Lithuania | 6.76 |
Ta karshe a jerin ita ce kasar da yaki ya tagayyara Afghanistan. A wani bayanin, a cikin kasashe 137, ita ce kasa mafi rashin farin ciki. Bayan ita akwai Lebanon, Sierra Leone, Zimbabwe da Congo, da ke a matakin biyar din farko na kasashe marasa farin ciki a duniya.
Daga ta shida zuwa 10 akwai Botswana, Malawi, Comoros, Tanzania da Zimbabwe.
Asali: Legit.ng