Matashi Yana Aji 3 a Jami’a Ya Gano Cewa Sunansa Baya Rijistar Jami’a

Matashi Yana Aji 3 a Jami’a Ya Gano Cewa Sunansa Baya Rijistar Jami’a

  • Tsokaci da dama ya biyo bayan bidiyon wani matashi da ya ce ya gano babu sunansa a rajistan jami'arsa bayan shekaru 3 da shigarsa
  • Mutum ya bayyana yadda yayi karatu a Jami'ar Najeriya ta Nsuka, UNN sannan ya gano lamarin mai ban mamaki ne yana mataki na uku a jami'ar
  • Bayyana abun da ya faru da yayi ya janyo tambayoyi masu ban mamaki a zukatan 'yan dandalin TikTok, inda wasu suka ce hakan ba abun mamaki bane a Najeriya

Wani matashi ya bayyana yadda ya gano yana shekararsa ta uku cewa sunansa baya cikin rijistan jami'arsa. Mutumin ya fadi hakan ne a wani bidiyon tattaunawa da Arrow House Studios suka wallafa a TikTok.

Matashi a Jami’a
Matashi Yana Aji 3 a Jami’a Ya Gano Cewa Sunansa Baya Rijistar Jami’a. Hoto daga Marko Geber and Klaus Vedfelt/Getty Images.
Asali: Getty Images

A faifan bidiyon da ya dauki tsawon minti daya, matashin ya bayyana yadda yayi karatu a Jami'ar Najeriya ta Nsukka, na tsawon shekaru uku kafin ya yanke shawarar canza fannin karatu.

Kara karanta wannan

Kada Ku Bar Najeriya a Hannun ‘Yan Ta’adda, Gwamnan Binuwai Ya Roki Jami’an Tsar

Yazo canza fannin karatunsa daga 'Kidaya zuwa Kimiyyar Na'ura mai kwakwalwa, daga nan ne ya gano cewa makaranta bata san da zamansa ba.

Wasu 'yan Najeriya suna ta cewa irin wannan abun yana yawan faruwa a jami'oin Najeriya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yayin da wasu suka sanya alamar tambaya game da matashin, suna tambayar ko dai ba a bashi lambar shiga jami'a ba a lokacin da ya shiga.

Tsokacin jama'a

@strikkergrills:

"Hala dai baka amsar sakamakon jarabawar karshen zango ne ba? Ko ba a fidda jerin sakamakon jarabawarku?

@BLACKTRUTH yayi tsokaci:

"Haka UNN suke yi."

@SIR_BLAQ001 yayi tsokaci:

"Wata kawata ta kammala fannin karatu na tsawon shekaru hudu a Unical, yayin da ya kamata su kammala karatun, makarantar take fada musu wai ba a tantance fannin karatun ba."

@Kels Koch ya ce:

Kara karanta wannan

Hotunan Amarya da Ango a Adaidaita Sahu Zasu Coci Daura Aurensu ya Janyo Cece-kuce

"Irin haka ne ya faru da ni abun dariya aji na karshe a ESUT."

@Peterfrank ya ce:

"Zamani na bada labari mai bacin rai amma yanzu ya wuce. Na fahimci yadda ya ji."

@StoryBoom21 tayi tsokaci:

"Sun kusan yi min haka, amma Ubangiji yafi karfin UNAD."

@Redemptiom Edegbe ya ce:

"Hakan yayi kama da labarin kanzon kurege."

@Carsonv yayi tsokaci:

"Sama da kashi 30 na injiniyoyin dalibai na shekararmu suna da takardar shaidai shiga makaranta na jabu a lokacin. Ciwa-ciwa ta shiga makaranta a lokacin tayi yawa."

Ango da Amarya sun bayyana wurin bikinsu a Napep

A wani labari na daban, wasu masoyan juna sun bayyana a wurin daurin aurensu a adaidaita sahu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng