Zamanin Sarauniya Elizabeth Ya Wuce, an Fito da Kudi Mai Hoton Danta, Sarki Charles
- Kasar Ingila ta yi sabon kudi mai dauke da hoton sabon Sarki Charles da ya gaji sarautar mahaifiyarsa, sarauniya mai dogon zamani
- Allah ya yiwa sarauniyar Ingila Elizabeth II rasuwa a watanni baya da suka shude, ana jiran sauye-sauye da za su biyo baya
- Babban bankin kasar ya bayyana lokacin da za a fara amfani da kudin, da kuma yadda za a yi tsoffin kudaden kasar
Landan, Ingila – Nan gaba kadan Ingila za ta yi sallama da kasha kudi mai hoton marigayiya sarauniya Elizabeth, an buga sabon kudi a kasa.
A cewar rahoton BBC Hausa, tuni aka buga fam biyar, 10, 20 da 50 masu dauke da hoto, Sarki Charles da ya gaji sarautar kasar.
Wannan sauyi dai babban bankin Ingila ne ya samar dashi watanni kadan bayan mutuwar sarauniya mai dogon zamani.
Yaushe za a fara kashe kudin?
Bankin ya kuma bayyana cewa, kudaden za su fara yawo a cikin mutane ne daga tsakiyar shekarar 2024 ga mai rai, haka nan New York Times ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A hoton kudin da muka gani, za ku iya ganin hoton sarki Charles da kuma wasu tsarmin tsaro da aka yi a jikin kudaden.
Bankin ya ce, a yanzu dai tsoffin kudi masu hoton sarauniya ne za su ci gaba da yawo a kasuwanni da hannun jama’a, ko da kuwa an fara amfani da sabbin bugun.
Sarauniya Elizabeth ce wacce aka fara sanya hotonta a kudin takarda na Ingila a 1960, kuma itace sarauniyar da tafi dadewa a gadon sarauntar kasar.
Sauya sarauniyar a jikin kudin kasar na daya daga cikin abubuwan da jama’a ke jira tun bayan mutuwar.
A yanzu dai Sarki Charles ne sarkin Ingila, kuma za a fara kashe kudin kasar mai dauke da hotonsa kamar yadda aka yi tsammami.
Elizabeth II: Za a Kashe Kusan Naira Biliyan 4 Wajen Bikin Jana’izar Sarauniyar Ingila
A wani labarin kuma, kun ji cewa, an ce kusan Naira biliyan 4 ake tunanin kashewa lokacin da aka sanar da jana'izar Sarauniyar Ingila.
Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan da masarautar ta sanar da mutuwar sarauniyar.
An yi shagali da jimami hade da koke-koken binne sarauniya a kasar Ingila.
Asali: Legit.ng