Yadda Jikan Sarauniya Elizabeth II Ya Gaji Tamfatsetsen Gidanta Mai Darajar N426b
- Yarima William, babban yayan yarima Harry sune 'ya'ya biyu da Sarki Charke ya haifa tare da marigayiya Diana
- Bayan mutuwar sarauniya Elizabeth II, mahaifin Yarima William ya gaji karagar mulkin wanda hakan yasa William ya zama yarima mai jiran gado
- Sarkin goben da 'dan uwansa basu jituwa wanda hakan yasa Harry a ajiy mukaminsa na gidan saraunta tare da barin UK baki daya
'Dan Sarki Charles, Yarima William ya gaji wani tamfatsetsen gidan marigayiya Sarauniya Elizabeth II mai darajar N426 biliyan.
Sarkin gobe
Yarima William wanda aka nada a matsayin mai jiran gadon sarautar Ingila ya gaji katafaren gidan Duchy na Cornwall daga mahaifinsa wanda ya hau karagar mulkin bayan mutuwar sarauniyar mai tsawon kwana.
Katafaren gidan yana da wasu kadarori da suka hada katon fili dake kudu maso yammacin Ingila wanda ke da kiyasin kadada 140,000.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Sarki Edward ne farko ya mallaki wannan katon gidan a 1337 kuma yana da darajar kusan N214 biliyan kamar yadda bayanai suka nuna.
Kamar yadda CNN tace, ana mafni da kudin da rukunin gidajen ke samarwa wurin ayyukan sadaka da taimako.
Malami a jami'ar Lancaster mai suna Laura Clancy wanda ya wallafa wani littafi kan kudaden gidan sarauta inda yace:
"Wasiyyar jinin sarauta a boye suke, don haka ba mu san mene ne a ciki ba kuma mene ne darajarsu kuma ba a taba saninsu."
A 2021 Forbes ta kiyata dukiyar marigayiyar ta kai biliyan sitti da miliyan dari biya da ashirin biyar na shillings.
Kyawawan Hotunan Lokuta da Rayuwar Marigayiyar Sarauniya Elizabeth II
A wani labari na daban, Ingila ta fada makoki a ranar Alhamis, 8 ga watan Satumban 2022 bayan labarin mutuwar sarauniya Elizabeth Alexandra Mary wacce ta kasance sarauniyar da ta fi kowanne sarki dadewa a kujerar sarautar Birtaniya.
Mahaifiya kuma kakar an haifeta a ranar 21 ga watan Afirilin 1926 a titin Bruton dake Landan, UK ga tsohon Duke din York, Yarima Albert da matarsa Elizabeth Bowes-Lyon.
Kamar yadda takardar da fadar Buckingham ta fitar ta bayyana,sarauniyar ta tabbata basarakiyar da tafi dadewa a kujerar tun a 2015 yayin da ta wuce shekarun da Sarauniya Victoria tayi a kujerar.
Asali: Legit.ng