Bidiyo: Gwamnatin Saudiyya Ta Damke Wanda Yaje Umrah Don Sarauniya Elizabeth
- Wani Balarabe ya shiga harami gabatar da aikin Umrah don marigayiya Sarauniya Elizabeth II
- Jami'an tsaron Masallacin Harami sun cika hannu da shi kuma sunce zai gurfana gaban kuliya
- Duk da cewa ya halasta ayi umrah don wani, hakan bai halasta ga wanda ba Musulmi ba
Hukumomi a kasar Saudiyya sun damke wani mutumi da yayi ikirarin ya yi tattaki zuwa Makkah don yin aikin Umrah a madadin marigayiya Sarauniya Elizabeth II.
Mutumin dan kasar Yemen, a ranar Litnin ya wallafa bidiyon kansa a soshiyal midiya yana filin Harami.
Rike da wata farar riga da rubutu a kanta, ya yi addu'an Allah a jikan Sarauniya Elizabeth.
A rubuce kan rigar:
"Ina Umrah don Saraunia Elizabeth II, muna rokon Allah ya karbeta cikin salihan bayi."
Adamawa: An biyashi N5000 da kwanon Shinkafa 4 don yayi kisan kai, ya kashe mutum 1, ya bar daya na jinya
Bidiyon ya yadu a kafafen sada zumuntan Saudiyya inda mabia Tuwita suka bukaci a damkesa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Gwamnatin kasar Saudiyya ta haramta zanga-zanga ko rike hoton wani don kamfe a cikin Haramin Makkah.
Duk da cewa ya halasta ayi umrah don wani Musulmi da yai mutu, hakan bai halasta ga wanda ba Musulmi ba irin Sarauniyar Elizabeth.
An damkeshi
Jami'an tsaron Haramin Makkah sun damke mutumin wanda dan kasar Yemen ce, rahoton TRT.
Kafar yada labaran Saudiyya a ranar ta bayyana cewa:
"An damke wani dan kasar Yemen mazauni Saudiya wanda ya bayyana a bidiyo yana rike da tsumma cikin harami, hakan ya sabawa dokokin yin Umrah."
"An damkeshi kuma za'a wanzar da hukunci doka kansa."
Kalli bidiyon:
Sarauniyar Ingila, Elizabeth II Ta Rasu Tana da Shekaru 96
Kun ji labarin rasuwar sarauniyar Ingila Elizabeth II bayan 'yar gajiriyar rashin lafiya da aka sanar ta yi ranar Alhamis 8 ga watan Satumba.
Rahotanni daga majiyoyi sun shaida cewa, masarautar Ingila ta tashi bakin labarin jirkicewar lafiyar sarauniya, lamarin da yasa likitoci ke kai komo a kanta.
A wata sanarwar da masarautar ta Ingila ta fitar, an sanar da rasuwar sarauniyar da yammacin Alhamis.
Asali: Legit.ng