Yadda Wani Ma’aikacin Gidan Talbijin Ya Yi Murnar Mutuwar Sarauniyar Ingila A Shirin Kai Tsaye
- Ba kowa ne ya shiga kaduwa da alhini ba a duniya bayan samun labarin mutuwar Sarauniya Elizabeth ta kasar Ingila
- Wani ma’aikacin gidan talabijin na kasar Argentina ya bude kwalbar lemu a shirin kai tsaye don murnar mutuwar Sarauniya Elizabeth
- Wannan mai gabatar da shirin ba shi kadai bane ya fito fili ya nuna farin cikinsa a kan mutuwar sarauniyar ba a fadin duniya
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Buenos Aires – Yayin da fadar Buckingham ta sanar da labarin mutuwar Sarauniya Elizabeth II, wani ma’aikacin gidan talbijin na kasar Argentina, Santiago Cúneo ya bude lemun kwalba a shirin kai tsaye yayin da yake sanar da labarin mutuwar basarakiyar ta Ingila.
A wani bidiyo daga shirin kai tsayen, dan jaridan na kasar Argentina ya kasance kewaye da kayan alatu mai launin fari da shudi – kalar tutar Argentina – yana bude kwalbar lemu ga kuma kayan makulashe a gabansa.
Newsweek ta rahoto cewa Cúneo ya sanar da labarin mutuwar Sarauniya Elizabeth II da kalamai marasa dadi, yana mai cewa “tsohuwar banzar ta mutu. Ta tafi kowa ya huta. A tapawa shaidan wanda ya dauketa a karshe.”
Nan take wannan sanarwa mai cike da takkadama da dan jaridan na Argentina yayi ya yadu a kasar, inda ma’udu’in #Cuneoalmediodia ya fara tashe a Twitter.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Mutanen Argentina da dama sun caccaki Cúneo da wadanda ke goyon bayan abun da ya aikata a shirin talbijin.
Wani mai amfani da Twitter ya rubuta:
“Ni dan Argentina ne kuma wannan gayen baya wakiltana. Muna masu tausayawa kan wannan rashi.”
Yayin da dan jaridan ya yi murnar mutuwar basarakiyar mai shekaru 96, gwamnatin Argentina ta wallafa wani sakon ta’aziyya sannan ta ce kasar na tare da mutanen Ingila da ahlinta a wannan lokaci da jimami,’ a cewar jaridar The New York Post.
Daily Mail ta rahoto cewa wannan ba shine karo na farko da Cúneo ke haddasa cece-kuce ba. An kore shi daga gidan talbijin na Cronica a 2019 bayan da aka zarge shi da yada wani akida na Yahudawa.
An zargi Cúneo da yada akidar kasar Yahudawa a Argentina.
Argentina da Ingila sun fafata kazamin yaki a kan tsibirin Falkland a shekarar 1982, inda a karshe Argentina ta sha kaye.
A Sauya Sunan Aso Rock Ko Sauran Yankunan Arewa Zuwa Sunan Sarauniya Elizabeth, Ohanaeze Ga FG
A wani labarin, kungiyar Inyamurai ta Ohanaeze Ndigbo, ta bukaci gwamnatin tarayya da ta yi watsi da kiran da aka yi mata na sauyawa jami’ar Najeriya ta NSUKKA suna zuwa na Marigayiya Sarauniyar Ingila.
A cewar kungiyar wannan yunkuri zai fi dacewa ne da fadar shugaban kasa wato Aso Rock a Abuja ko kuma sauran yankunan arewacin kasar, jaridar Punch ta rahoto.
Hakan na zuwa ne bayan kungiyar ta jadadda cewa lallai sai tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Young Progressives Party, Adamu Garba, ya baiwa yan kabilar Igbo hakuri a kan wannan furuci da ya yi.
Asali: Legit.ng