Budurwa ta kai karar magidanci wurin matarsa bayan yayi mata karyar mutuwar matarsa

Budurwa ta kai karar magidanci wurin matarsa bayan yayi mata karyar mutuwar matarsa

  • Dani Bose tauraruwa ce a TikTok wacce ke samun makuden kudi wurin gwada samarin 'yan mata wadanda ba a yarda da su ba
  • Wata mata ta tunkari Bose da bukatar ta gwada mata mijinta wanda suka yi shekaru 30 da aure ko yana cin amanarta a bayan fage
  • Dani ta sanar da matar yadda mijinta ya neme ta da lalata, ya yi karyar shekaru tare da yin ikirarin cewa matarsa ta sheka lahira

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Dani Bose, kyakyawar Baturiya ta fallasa wani mutum da suka kwashe shekaru 30 da matarsa da aure amma yake neman matan banza a waje.

Dani Bose
Karuwa ta kai karar magidanci wurin matarsa bayan yayi mata karyar mutuwar matarsa. Hoto daga Dan Bose
Asali: UGC

Ya yi ikirarin cewa matarsa ta mutu

Budurwa mai shekaru 21 kuma tauraruwa TikTok ta bayyana yadda magidancin yayi ikirarin cewa matarsa ta mutu kuma yake son su hadu domin lalata.

Kara karanta wannan

Bantaba sanin ina da ciki ba: Budurwa mai shafaffen ciki ta haihu a bandaki

A bidiyon, ta bayyana yadda matarsa ta neme ta kuma tace tana son ta gwada mata cewa ko mijinta da suka yi shekaru 30 suna tare yana cin amanarta.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ta rubuta: "Barka dai, diyata ta nuna min ire-iren bidiyoyin ayyukanki a soshiyal midiya. Zan so sanin farashin ki da kuma yadda zaki gwada mijina."

Kamar yadda New York Times ta ruwaito, magidancin ya nemi Bose da lalata kuma ya zabga karyar shekarunsa tare da yin ikirari cewa matarsa ta mutu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng