Yanzu-yanzu : Tsohon Firai ministan Japan Da Aka Harba A Gangamin Yakin Neman Zabe Ya Mutu
- Tsohon Firayim Ministan kasar Japan da aka harba a kirji a gangamin yakin neman zabe ya Mutu
- Jami'an tsaro sun samu nasarar kama wanda ya harbe tsohon firaministan kasar Japan din da ya mutu
- Shinzo Abe shine Firai ministan da ya fi dadewa a akan karagar mulkin kasar
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Japan - Tsohon Firayim Ministan Japan, Shinzo Abe, wanda aka harbe shi a lokacin da yake jawabi gabanin zaben majalisar dattawa da za a yi a ranar Lahadi, ya mutu. Rahoton Daily Trust
An harbi Abe a kirji da wuya a yammacin ranar Alhamis a birnin Nara.
Ya fadi ne a kan titi, inda jami’an tsaro da dama suka ruga zuwa gare shi, a cewar jaridar Guardian UK.
Kamfanin dillancin labarai ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na NHK cewa, babban jami’in jam’iyyar Liberal Democratic Party, yace Abe ya rasu ne a asibitin da yake jinya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hotuna da bidiyo sun nuna yadda jami'an tsaro suka tunkari dan bindigar wanda yanzu haka yake hannun 'yan sanda.
Harin da aka kai kan Abe, wanda shi ne firayim minista mafi dadewa a kasar Japan, ya girgiza kasar.
Tun da farko, Firayim Minista Fumio Kishida ya yi Allah wadai da matakin a wani taron manema labarai, inda ya kara da cewa, “Abe na cikin mawuyacin hali. Ina addu'ar ya tsira."
Matan tsohon fitaccen mawaki Eedris Abdulkareem zata bashi kodanta
Jihar Legas - Wani na kusa da iyalan mawaki Eedris Abdulkareem ya shaida wa jaridar TheCable Lifestyle cewa matar mawakin ta dauki nauyin ba wa mijinta kodarta bayan an kammala yi masa dukkan nau'ikan gwaje-gwaje.
Abdulkareem, tsohon shahararren mawakin Najeriya, yana fama da ciwon koda.
Asali: Legit.ng