Nayi asarar kuɗina: Matashi na sharɓar kuka bayan budurwar da ya kashewa N2.1m kan karatu tayi watsi da shi

Nayi asarar kuɗina: Matashi na sharɓar kuka bayan budurwar da ya kashewa N2.1m kan karatu tayi watsi da shi

  • Wani mutumi 'dan kasar Kenya ya karade ko ina a yanar gizo, inda aka ganshi a wani bidiyo yana kuwwa iya karfinsa tare da kiran sunan wata mata da ya yi wa lakabi da tauraruwa mai wutsiya data tatse masa sulalla
  • A cewar mutumin da ba a gano sunansa ba, mayaudariyar ta 'warwara daga hannunsa' Ksh 620,000 (N2.1 miliyan) wanda ya yi amfani da shi wajen daukar nauyin karatunta har ya rage saura watanni 2 ta kammala
  • Maza da dama a yanar gizo sun yi Allah wadai da irin kururuwar da ya yi, yayin da wasu suka ganin ya kamata wasu su koyi darasi a nan su daina biya wa 'yan mata kudin makaranta

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kenya - Wani mutumi 'dan kasar Kenya ya bar mutane a yanar gizo baki bude bayan bidiyonsa ya bayyana yana kururuwa bayan wata mata da ya dauki nauyin karatunta tayi watsi da shi.

Kara karanta wannan

Babbar Sallah: Ba zam huta ba har sai na samar da sassauci ga yan Najeriya, Shugaba Buhari

Wata mai amfani da shafin Facebook, Betty Opondo, ne ta wallafa bidiyon da ya karade yanar gizo wanda ya dauki tsawon dakika 30 na mutumin wanda ya yi tsokaci tare da cewa ya kamata mutane su kai kansu makaranta.

Matashi
Nayi asarar kuɗina: Matashi na sharɓar kuka bayan budurwar da ya kashewa N2.1m kan karatu tayi watsi da shi. Hoto daga Betty Opondo
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce ya dauki nauyin karatun wata mata wacce tayi watsi da shi ana saura watanni ta kammala karatunta.

A bidiyon, an ji yadda mutumin ke kuwwa tare da ihu yana cewa: "Na yi zaton na aka da motoci guda, yanzu gashi nan ina fama da kudin da zan biya haya."
"Wannan matar ta yanke shawarar lashe min sulalla yanzu da ya rage mata watanni biyu kacal ta kammala karatunta (ya fadi cikin kuka). Ta lashe min kudade."

Wallafar da matar tayi ya matukar ba wa masu amfani da shafin sada zumuntar zamani mamaki, inda wasu suke shawartar maza da su yi hattara da biya wa matan da suke soyayya da su kudin makaranta.

Kara karanta wannan

Fashin magarkamar Kuje: FG ta fitar da bayanan 'yan Boko Haram din da suka tsere

Jama'a sun yi masa martani

Tsokacin jama'a:

Obang'e Rollance Otuom Polo ya ce: "Wannan mutumin baya halartar majalisar tattaunawar maza, shiyasa ya dauki nauyin tauraruwa mai wutsiyar."
Apelez Mike ya ce: "Maza da dama na can suna kokawa kan kudinsu."
Akoko Jambita ya yi tsokaci: "Wannan shi ne yadda muke yi, mun daina kuka a boye yanzu."
Jeremy Akn ya ce: "Amma mata wani lokaci su suke kusanto da lokacin mutuwarsu."
George Owala ya ce: "Amma wannan ya cika sakarai. Ya kamata ya yi shiru ya jira lokacin daukar fansa don ya rama abun da tayi masa."

Asali: Legit.ng

Online view pixel