Wata Yar Najeriya Ta Mayar Da N14.9m Da Ta Tsinta Cikin Kujeru Da Aka Bata Kyauta, Ta Samu Tukwici

Wata Yar Najeriya Ta Mayar Da N14.9m Da Ta Tsinta Cikin Kujeru Da Aka Bata Kyauta, Ta Samu Tukwici

  • Wata mata yar Najeriya mai suna Vicky Umodu ta mayar da kudi N14.9bn ko $36,000 da ta tsinta cikin kujera da aka bata kyauta a shafin Craigslist
  • Matar wacce ke zaune a San Bernardio, California tana duba shafin na Craigslist ne don neman kujerar da za ta siya sai ta gano wasu na neman kyautar da nasu
  • Ta bukaci su bata kuma suka amince, sai daga baya ta gano makuden kudi a cikin kujerun kuma ta mayar wa wadanda suka bata kujeran

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Amurka - Vicky Umodu, wata yar Najeriya da ke zaune a San Bernardio, California ta nuna halin gaskiya da rikon amana bayan ta mayar da N14.9m da ta tsinta a kujera.

Umodu ta samu kyautan kujerun ne daga wasu mutane wadanda ke niyyar bayar da su kuma ta nema suka bata.

Kara karanta wannan

2023: Mace Guda Da Ke Takarar Shugaban Kasa a APC Ta Janye Wa Tinubu, Ta Bayyana Dalili

Wata Yar Najeriya Ta Mayar Da N149m Da Ta Tsinta Cikin Kujeru Da Aka Bata Kyauta, Ta Samu Tukwici
Yar Najeriya Ta Mayar Da N149m Da Ta Tsinta Cikin Kujeru Da Aka Bata Kyauta, Ta Samu Tukwici. Photo credit: Diseph Mgborogwu, Vicky Umodu and Bloomberg/Getty Images.
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda abin ya faru

Matar yar Najeriya mai gaskiya ta koma birnin California ne kuma ta ke duba shafin intanet na Craigslist domin ta siya sabon kujeru.

Daga nan ta gano wasu mutane suna son bada kyautan kujerun wani dan uwansu da ya rasu.

Ta tafi gidansu ta karbo kujerun ta kawo su sabon gidan ta. Da kujerun suka iso, tana duba su sai ta gano makuden kudi a cikin daya cikin kujerun.

Umodu ta ce:

"Ban dade da shiga gidan ba, kuma ba ni da komai a gidan. Na yi murna, don haka muka karbo kujerun muka shigo da shi gida.
"Ina fada wa da na, zo, zo zo! na fada da babban murya. "Wannan kudi ne! Ya kamata in kira mutumin!".

Ta mayar da kudin

Ta tuntubi mutanen da suka bata kujerun kuma ta mayar musu da kudin. Ta ce:

Kara karanta wannan

Yanzu nan: Masu neman kujerar shugaban kasa a APC sun ragu, an bar mutum 2 kacal

"Ubangiji ya yi min rahama ni da yara na. Dukkansu suna da rai da lafiya. Ina da kyawawan jikoki uku, don haka mene zan nema wurin Ubangiji?".

Bayan mayar da kudin, an bata tukwicin N900,000 saboda gaskiyanta.

Shafin @instablog9ja ne ta wallafa labarin.

Wasu mutane a Instagram sun tofa albarkacin bakinsu

@lulusmooth ta ce:

"Ni dai sai na rike kudin tsawon shekara guda kafin in mayar."

@poshest_hope cewa ta yi:

"Kamar yadda ya dace. Ba kudin ta bane."

@gucci_tos ta ce:

"Ta yaya za su ajiye wannan kudin mai yawa a cikin kujera idan ba gwada ta suke son yi ba."

Duk Da Na Yi Digiri Amma Yanzu Dakon Kaya Da Sayar Da Soyayyen Nama Na Ke YI: Matashi Ya Bayyana a Bidiyo

A wani rahoton, wani matashi dan Najeriya mai suna Dwomoh Emmanuel, ya tafi TikTok domin nuna sana'ar da ya ke yi akasin abin da ya karanta yayin digiri a jami'a.

Kara karanta wannan

Da duminsa: EFCC suna "aikin sirri" a filin zaben fidda gwani na APC, Majiya ta tabbatar

Matashin da ya yi digiri a bangaren kididdiga, ya wallafa wani bidiyo da ke nuna shi yana daukan kaya sannan yana sayar da soyayyen kaza a wani shago.

Mutumin ya dauki babban jaka a kansa. Wani sashi na bidiyon ya nuna shi yana soya wani abu da ya yi kama da fukafukin kaza.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: