An Zaɓi Ƴar Najeriya Matsayin Magajiyar Gari a Birtaniya

An Zaɓi Ƴar Najeriya Matsayin Magajiyar Gari a Birtaniya

  • Pauline Akhere George, yar asalin karamar hukumar Esan ta Gabas a Jihar Edo ta zama Magajiyar Garin Lambeth Borough a Birtaniya
  • Ms Akhere George ce mace ta farko, haifafiyar Najeriya da ta fara rike mukamin magajiyar garin Lambeth a tarihin kafuwar garin
  • A yayin bikin rantsar da ita, sabuwar magajiyar garin ta mika godiya na musamman ga wadanda suka zabe ta da kuma yan uwanta a gida Najeriya

Birtaniya - An zabi Pauline Akhere George, haifafiyar Najeriya kuma yar Birtaniya a matsayin magajiyar garin Lambeth Borough, Landan a Birtaniya na shekarar 2022/2023, rahoton Nigerian Tirbune.

Bayan zabenta, Ms George, yar asalin Okhuessan, daga karamar hukumar Esan ta Gabas a Jihar Edo ta zama mace na farko yar Najeriya da ta fara zama Magajiyar Lambeth Borough.

Kara karanta wannan

Da duminsa: An yi garkuwa da 'yar takarar APC ana tsaka da zaben fidda gwani

An Zaɓi Ƴar Najeriya Matsayin Magajiyar Gari a Birtaniya
'Yar Najeriya Ta Zama Magajiyar Gari a Birtaniya. Hoto: Nigerian Tribune.
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A wurin bikin rantsar da ita da aka yi a dakin taro na Lambeth, ta yi jinjina ga masu kada kuri'a da suka karrama ta suka zabe ta don yi musu hidima.

Jaridar ta Nigerian Tribune ta rahoto cewa tsohuwar mataimakiyar Magajiyar Garin na Lambeth na 2020/2021 ta kuma yi godiya ga yan uwanta da ke gida a Najeriya.

Mahaifiyar sabuwar magajiyar garin, gimbiya daga gidan sarauta na Alenkhe kwararren malamar jinya ne da ya yi karatu a South Columbia School of Nursing, England da Thames Valley University, England.

Ta kuma yi karatun digiri na biyu a bangaren aikin shari'a daga Jami'ar London Metropolitan.

Pauline ta dade tana ayyukan yi wa al'umma hidima a garin Lambeth Borough

Aunty Pauline, kamar yadda aka fi saninta, ta yi aiki a National Health Scheme (NHS) inda ta taimaki mutanen unguwarta lokacin COVID-19 kuma da wakilci malaman jinya a kotu a wurin aiki da kotun ma'aikata.

Kara karanta wannan

Emefiele yana nan: Ba mu san da labarin tunbuke Gwamnan babban banki ba inji CBN

Ta kuma yi ayyuka da suka shafi yaki da laifuka na wuka da bindiga da samar wa matasa ayyukan yi da karfafa musu gwiwa su koyon makamashin aiki.

Bayan rayuwa cikin daji yana cin ciyawa, yanzu wankan sutturu na alfarma ya ke yi, ana girmama shi a gari

A wani rahoton, wani matashi, Nsanzimana Elie ya kasance a baya ya na zama cikin daji saboda yanayin suffar sa, sannan mutanen kauyen sa har tonon sa su ke yi.

Akwai wadanda su ke kiran sa da biri, ashe daukaka ta na nan biye da shi, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

Mahaifiyar Elie ta ce Ubangiji ya amshi addu’ar ta na ba ta shi da ya yi bayan yaran ta 5 duk sun rasu, kuma ba ta kunyar nuna shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: