Yanzu-Yanzu: Buhari Ya Shilla UAE, Zai Gana Da Magajin Sheikh Khalifa bin Zayed Al Nahyan
1 - tsawon mintuna
Shugaba Muhammadu Buhari zai gana da sabon shugaban Hadadiyar Daular Larabawa, UAE, Sheikh Mohammed bin Zayed Al Nahyan, don mika ta'aziyarsa bisa rasuwar tsohon shugaban, Sheikh Khalifa bin Zayed Al Nahyan.
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
A cewar sanawar da kakakin Shugaba Buhari, Garba Shehu ya fitar a ranar Alhamis, shugaban kasar zai bar Abuja a ranar Alhamis, zai kuma yi amfani da damar don taya sabon shugaban murna, tare da karfafa dankon zumunci tsakanin Najeriya da UAE.
Saurari karin bayani ...
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng
Tags: