Ana dab da Iftar, magidanci a Saudiyya ya kone iyayensa, iyalinsa da gidansa kurmus
- Wani balarabe'dan kasar Saudi a Safwa, ya halaka mahaifinsa, mahaifiyarsa, 'dansa da 'diyarsa ta hanyar antayawa gidansa fetur, gami da banka musu wuta ana gab da buda baki
- Duk da yadda suka nemi dauki daga jama'an annabi, ba a samu damar ceto rayuwarsu ba, har sai da gawawwakinsu suka kone kurmus
- Sai dai, yayin da jami'an tsaro farar hula suka bincika musabbabin gobarar, sun gano yadda mutumin ya yi ta'ammuli da miyagun kwayoyi (Shabu) kafin ya halakasu da azumi a bakinsu
Safwa, Saudi Arabiya - Ana dab da buda baki, wani mutumi ya garkame mahaifinsa, mahaifiyarsa, 'dansa da 'diyarsa, wadanda ke azumi a gidan a Saudiyya gami da banka wa gidan wuta.
Yadda wutar ta fara
Wutar ta fara ci ne sanadiyyar man fetur da aka antaya wa gidan, gami da banka wa gidan wuta, wanda ya lashe rayukan mutane hudu: mahaifinsa, mahaifiyarsa, karamin yaronsa da 'diyarsa.
Mummunan lamarin ya auku ne a Safwa, kusa da Qatif, inda gobarar ta balle ana dab da buda baki.
Iyalin basu tsira daga kunar wutar ba, inda ya rufesu da gan-gan a wani daki don hana su guduwa.
Duk da irin neman agajin da suka yi, hakan bai sa sun tsira ba
Duk da sun nemi dauki daga jama'an Annabi, babu matakin da aka dauka wajen ganin an ceto rayuwarsu. Haka gawarsu ta kone kurmus, The Islamic Information ta ruwaito.
Jami'an tsaro sun dauki mataki
Bayan kashe gobarar, jami'an tsaro sun kama wanda ake zargin, wanda shi ne makusancin wadanda iftila'in ya fada wa. Yayin da masu bincike suke kokarin gane dalilin aukuwar rashin hankali irin wannan.
'Yan sanda sun mika mai laifin sashin gurfanarwan bayan damko shi, tare da kammala duk wasu matakai da suka dace akansa.
Meye dalilin gobarar?
An gano yadda wanda ake zargin ya yi ta'ammuli da wasu miyagun kwayoyi (Shabu), wanda ya yi sanadiyyar kwarkwancewarsa.
Yayin bincike da farko, an gano yadda aka garkamesu a daki daga waje.
Jami'an tsaro a kasar Saudi Arabia sun damke mabarata a Masjid Al-Haram
A wani labari na daban, jami'ai a kasar Saudi sun yi ram da mazauna da masu karya dokar da aka kama suna bara a Makkah, wadanda suka hada da cikin dukkan manyan masallatai 2 na Annabi, jaridar The Islamic Inforrmation ta ruwaito.
Kamar yadda hukumomin Saudi suka bayyana, an yi ram da wani mazaunin kasar 'dan kasar Indiya a harabar babban masallacin da wani 'dan kasar Morocco a wajen masallacin bayan an kamasu suna bara don su samu tausayawa daga masu bauta.
Asali: Legit.ng