Wani Mutumin Najeriya ya je da kafar dama, ya samu babban mukami a hukumar Amurka

Wani Mutumin Najeriya ya je da kafar dama, ya samu babban mukami a hukumar Amurka

  • Yemi Oshinnaiye zai zama babban jami’in da ke kula da bayanai a hukumar TSA a kasar Amurka
  • Mista Oshinnaiye zai dare wannan kujera a watan Mayu a dalilin ritayar mai gidansa, Russ Roberts
  • Abin ban sha’awar ita ce asalin Yemi Oshinnaiye mutumin Najeriya ne da ya tare a kasar Amurka

United States – A makon nan aka ji mutumin Najeriya, Yemi Oshinnaiye ya zama sabon babban jami’in kula da bayani na hukumar TSA a kasar Amurka.

Rahotanni da mu ka samu daga Federal News Network na Amurka sun bayyana cewa Yemi Oshinnaiye ya kai matsayin CIO a hukumar da yake aiki.

Kafin yanzu Mista Oshinnaiye ya rike mataimakin babban jami’in kula da bayanai a ma’aikatar kula da shige da fice da kula da katin zama ‘dan Amurka.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Tsohon na kusa da Buhari ya fice daga jam'iyyar APC, ya jero dalilai

Rahoton ya ce yanzu Oshinnaiye wanda asalinsa mutumin kasar Najeriya ya zama sabon CIO ne bayan wanda ke rike da mukamin, Russ Roberts ya sauka.

Russ Roberts zai bar ofis

Tun a karshen shekarar 2021 Russ Roberts ya rubuta takardar ritaya, sai yanzu zai sauka daga kujerar. Roberts ya dauki tsawon lokaci a wannan matsayi.

Kamar yadda mu ka ji labari, Roberts zai mika ragamar shugabancin TSA ga Oshinnaiye a farkon watan Mayun nan, domin ya cigaba daga inda ya tsaya.

Yemi Oshinnaiye
Yemi Oshinnaiye Hoto: www.meritalk.com
Asali: UGC

Wasu mukamai Oshinnaiye ya rike?

Tun watan Maris a 2019 ‘dan Najeriyar ya zama mataimakin Russ Roberts a hukumar ta TSA. Tsakanin 2012 da 2017, Oshinnaiye ya yi aiki ne a DHS.

Bayan gajeren lokaci yana aikin zaman kan shi, sai Oshinnaiye ya sake dawowa gwamnati. A lokacin da Oshinnaiye yake USCIS, ya kawo gyare-gyare.

Kara karanta wannan

Sakin Dariye da Nyame: Bayan kwashe shekaru 11 a kotu, da kashe miliyoyin kudi, Shikenan: Lauyoyin EFCC

Legit.ng Hausa ta fahimci sabon CIO din ya rike jami’in fasaha a wani kamfani mai suna Dev Technology Group, Inc. da ke Virginia na 'yan shekaru.

Bayanan da ke shafinsa na LinkedIn sun nuna ya yi digiri a harkar kasuwanci a jami’ar Georgetown a kasar Amurka daga shekarar 1993 zuwa 1997.

Oshinnaiye kwararren masanin kimiyya da fasahar zamani ne wanda kuma yake da idanu a fannin kirkirar manhajoji, horaswa, shugabanci da kasuwanci.

Betty Anyawu za ta je Majalisa?

Dazu aka ji cewa gwamnan jihar Ondo, Oluwarotimi Akeredolu ya bayyana goyon bayan shi ga mai dakinsa, Betty Anyawu na neman Sanata a zaben 2023.

Uwargidar gwamnan Ondo ta na so ta yi takarar kujerar Majalisar Dattawa a inda ta fito, gabashin jihar Imo. Watakila za tayi takara a karkashin jam'iyyar APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel