Bidiyon Wasu Mutane Biyu Da Suka Bawa Hammata Iska a Masallacin Ka'aba

Bidiyon Wasu Mutane Biyu Da Suka Bawa Hammata Iska a Masallacin Ka'aba

  • Wasu mutane biyu masu cikin masu ibada sun bawa hammata iska a cikin Masallacin Harami na Makkah mai tsarki
  • Jami'an tsaro na musamman masu kula da aikin Hajji da Umarah a Saudiyya sun kaddamar da bincike kan afkuwar lamarin
  • Jami'an tsaron sun kuma yi kira ga dukkan masu ibada da su rika mutunta alfarmar masallatai biyu masu tsarki a Makkah su kuma rika ibada cikin natsuwa

Saudiyya - Jami'an tsaro na musamman masu kula da aikin Hajji da Umarah a kasar Saudiyya sun fara bincike a kan wasu mutane biyu da suka yi dambe a cikin Massallacin Harami na Makkah, BBC Hausa ta rahoto.

Wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta ya nuna wasu mutane biyu suna bawa hammata iska a cikin masallacin Makkah, a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Hotunan Kafin Aure Na Wata Zankadediyar Budurwa da Angonta Karami Ya Ja Hankali

Bidiyon Wasu Da Suka Bawa Hammata Iska a Masallacin Ka'aba
Wasu mutane biyu sun dambacce a Masallacin Ka'aba. Hoto: BBC Hausa.
Asali: Twitter

Jami'an tsaro sun yi karin bayani

Jami'an tsaro da ke kula da masu aikin Hajji da Umarah sun yi karin haske game da afkuwar lamarin a cikin wata sanarwa wacce ke cewa:

"Jami’an tsaro na musamman da ke kula da masu aikin Hajji da Umarah a Saudiyya sun fara bincike kan faɗa da ya ɓarke tsakanin wasu mutane biyu a wurin da ake Safa da Marwa da ke cikin Masallacin Harami na Makkah a ranar Alhamis."
"Babu rahoton cewa wani ya jikkata sakamakon fadar da suka yi amma an dauki matakai na shari'a dangane ga mutanen biyu, rahoton jaridar Saudi Gazette."

Sanarwar ta cigaba da cewa:

"Jami'an tsaron na muamman da ke kula da Hajji da Umarah sun bukaci masu ibada su rika mutunta alfarmar Ka'aba, kuma su kasance cikin natsuwa a yayin da suke yin ibadah a masallatai biyu masu alfarma a Saudiya."

Kara karanta wannan

Zambar Daukan Aikin Immigration: Kotu Ta wanke Abba Moro, ta kama Sakatariya da laifi

Ga bidiyon yadda abin ya faru a kasa:

Saurar karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164